Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Haram 2, Sun Kama Wasu 8 A Borno

[ad_1]

Dakarun Rundunar Haɗin Gwuiwa ta Arewa-Maso-Gabas (Joint Task Force) ƙarƙashin Operation Haɗin Kai (OPHK), a cikin shirin Operation DESERT SANITY V, sun yi nasarar daƙile wani shirin ƙwanton ɓauna da ƴan Boko Haram/ISWAP suka tsara a yankin Sambisa da Mandara Mountains a ranar Alhamis, 22 ga Janairu, 2026.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a safiyar Juma’a a Maiduguri, ya ce ƴan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari ta amfani da bama-baman da aka binne a gefen hanya (RSIED) da kuma ruwan wuta (harbi) mai ƙarfi. Sai dai dakarun sashi na 1 sun mayar da martani da  cikin ƙwarewe, inda suka kashe ƴan ta’adda 10, ciki har da manyan kwamandoji biyu da aka bayyana sunayensu da Basulhu da Ubaida.

  • Sojoji Sun Gano Ƙungiyar Safarar Makamai A Taraba
  • Sojoji Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’adda Munzir, Sun Kama Wasu 34 A Borno

Sanarwar ta ce bin sawunsu da aka yi bayan artabun ya haifar da ƙwato makamai da kayan aiki da dama, ciki har da bindigogi AK-47 guda uku, da bindigar pump-action guda ɗaya, da babura biyar, da gurneti guda biyu, da rediyon Baofeng guda biyu, da sinƙin harsashi 12 na AK-47, da na’urar harba roka (RPG charger), da igiyoyin tayar da bam, da batura, da bandoliya, da jakunkunan ruwa (camel bags), da kuma kayan haɗa bama-bamai.

A wani ɓangaren kuma, dakarun sashi na 1 sun sake yin arangama da ƴan ta’adda a yankin Malkube, inda suka kashe wasu biyu tare da ƙwato ƙarin bindigogi, da harsasai da na’urorin sadarwa ba tare da asarar rayukan dakarun ba.

Sojoji

Sanarwar ta ƙara da cewa wata ƙungiyar yaƙi ta Sashen 1 ta kuma dakile yunƙurin shigowar ƴan Boko Haram/ISWAP daga Kamaru ta yankin Galakura zuwa Nijeriya, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin a kiɗime. An kuma ƙwato babura biyu da wasu kayayyaki.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *