Kwamishina ya buƙaci mataimakin Gwamnan Kano ya yi murabus daga muƙaminsa




Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce zai fi dacewa mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi murabus daga muƙaminsa matuƙar ba zai goyi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Waiya, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Muhasa da ke Kano.

Ya yi wannan kalamai ne kan rahotannin da ke cewa mataimakin gwamnan ya yanke shawarar ci gaba da biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa gwamna Abba ya sauya sheƙa zuwa APC.

A cewarsa, saɓani a cikin gwamnati na iya haifar da rashin jituwa da rage tasirin shugabanci.

“Abin da muke fata, kamar yadda muka ga wasu kwamishinoni da ba su gamsu ba suka yi murabus, shi ma mataimakin gwamna ya ɗauki mataki idan ba ya tare da gwamna,” in ji Waiya.

Ya ce gwamnati tana buƙatar haɗin kai da manufa ɗaya domin samun nasara.

“Idan kana zaune a taron majalisar zartarwa ana tattauna yadda za a gina Kano, amma ana da shakku kan inda abubuwan da aka tattauna za su kai, to akwai matsala. Shugabanci yana buƙatar amana,” in ji Waiya.

Waiya, ya yi nuni da cewa wataƙila wani shirin siyasa ne ke tasiri kan matsayar mataimakin gwamnan, inda ya ce siyasar Kano cike take da gasa.

“Mutane da dama suna da burin zama gwamna. Babu laifi a yi gasa, amma idan buƙatu suka fara karo da alƙiblar gwamnati, mafi alheri shi ne mutum ya yi murabus ya je ya yi siyasarsa a bayyane,” in ji shi.

Sai dai ya ce hukuncin ƙarshe yana hannun mataimakin gwamnan.

“Shawara tana hannunsa. Idan ya ga zai iya ci gaba da aiki tare da gwamna a halin da ake ciki, babu matsala. Amma da ni ne, da na ajiye muƙamin na fuskanci tafiyata ta siyasa kai-tsaye,” in ji Waiya.

Ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da mayar da hankali kan ci gaban Kano.

“Abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne Kano. Duk wanda muradinsa ya ci karo da wannan manufa ba za a bari ya kawowa tafiyar gwamnati cikas ba,” in ji shi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *