Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwarorinsa Na Afghanistan Da Holland
[ad_1]
A jiya Juma’a, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho tare da takwarorinsa na kasashen Afghanistan da Holland.
Yayin zantawar ministan wajen kasar Afghanistan Mawlawi Muttaqi, ya gaya ma Wang Yi cewa, kasarsa na godiya ga kasar Sin bisa kokarinta na sulhunta Afghanistan da Pakistan.
A nasa bangare kuwa, Wang Yi ya ce, a lokacin da ake fuskantar karin rikice-rikice a duniya, ya kamata kasashe makwabta su kara hadin kai wajen tinkarar matsaloli daban daban, da nemo hanyar tabbatar da tsaronsu na bai daya.
Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin tana daukar matsayi na adalci, da na rashin karkata ga wani bangare, yayin da take sulhunta Afghanistan da Pakistan, tana kuma fatan ganin bangarorin 2 sun yi kokarin samun natsuwa da yin hakuri, sa’an nan su koma teburin shawarwari, don tabbatar da damar tsagaita bude wuta cikin sauri, da daidaita sabanin ra’ayi ta hanyar tattaunawa.
Ban da haka, ministocin 2 na Sin da Afghanistan, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa masu alaka da yakin da ake yi a kasar Iran, inda Wang Yi ya ce kasar Sin na son yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa, a kokarin gaggauta maido da zaman lafiya a yankin da kasar Iran ke ciki.
Ban da haka, duk dai a jiya Juma’a, Wang Yi ya tattauna da ministan wajen kasar Holland Tom Berendson, inda jami’an biyu suka jaddada aniyar kasashensu ta karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, kafin daga bisani suka yi musayar ra’ayi kan batun da ya shafi yakin da ake yi a kasar Ukraine. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link