Gidauniya ta tallafa wa mutum 38 da Naira miliyan 2.35 a Gombe
[ad_1]
Gidauniyar Zakka da Wakafi a Jihar Gombe, ta raba Naira miliyan 2.35 ga mutane 38 marasa galihu domin tallafa musu a lokacin watan Ramadan.
Tallafin na daga cikin ƙoƙarin da gidauniyar ke yi na taimaka wa mata da matasa su samu sana’o’i da dogaro da kai.
Shugaban gidauniyar, Dokta Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce an kafa gidauniyar ne domin amfani da zakkar Musulunci, sadaka da waƙafi wajen rage talauci da kuma taimaka wa marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Ya bayyana cewa tun a shekarar 2017 wasu masana a Jihar Gombe suka fara tattaunawa kan yadda za a tsara tsarin zakka domin taimaka wa marasa galihu.
Daga baya aka yi wa gidauniyar rijista da Hukumar Kula da Kamfanoni (CAC) a shekarar 2019.
Lamido, ya ce manufar gidauniyar ba kawai raba kuɗi ba ne, tana son mutane su koyi sana’a su zama masu dogaro da kansu.
“Manufarmu ita ce mu taimaka wa mutane su tashi daga masu karɓar tallafi su zama masu bayarwa a nan gaba,” in ji shi.
Tun bayan kafuwarta, gidauniyar ta gudanar da shirye-shirye da dama kamar tallafin karatu ga ɗalibai marasa galihu, taimakon marayu, rabon kayan abinci, da kuma horar da mata sana’o’i.
A bana, gidauniyar ta kammala zagaye na tara na shirin tallafa wa mata domin su fara sana’o’i.
Haka kuma ta shirya shan ruwa da marayu da marasa galihu, tare da rabon kayan abinci ga masu buƙata.
Gidauniyar ta kuma fara wani sabon shiri na kai abincin buɗa-baki zuwa asibitoci domin taimaka wa marasa lafiya da masu kula da su.
A wajen rabon tallafin, Madakin Gombe, Alhaji Umar Abubakar, da Injiniya Ibrahim Kawuwa, shugaban kwamitin shirya taron, sun yaba da ƙoƙarin gidauniyar.
Sun kuma roƙi al’umma musamman masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafawa irin waɗannan ayyukan alheri domin taimaka wa marasa galihu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link