Tinubu Da Kwankwaso Za Su Gana Yayin Da Siyasar Kano Ta Ɗauki Sabon Salo
[ad_1]
Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da jagororan Kwankwasiyya ‘, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yayin da siyasar Jihar Kano ke ci gaba da ɗaukar hankali.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Tinubu ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
- 2027: NNPP Za Ta Yi Nasara A Kano Ko Babu Gwamna Abba — Jigon NNPP
- Shugaban NAHCON Ya Kammala Ziyarar Aiki Ta Biyu A Shirye-shiryen Aikin Hajjin Bana
Jaridar Politics Digest ta ruwaito cewar Gwamna Abba ne ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya ganawar, a wani yunƙuri na Shugaban Ƙasa na haɗa kan manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.
A baya, Kwankwaso ya ƙi amincewa da komawa jam’iyyar APC tare da roƙon Gwamnan Kano kada ya fice daga NNPP.
Amma a ’yan makonnin nan, abubuwa na ci gaba da sauyawa.
A wata hira da manema labarai, Kwankwaso ya ce zai iya la’akari da wasu abubuwa kafin komawa APC idan aka bayyana masa matsayinsa.
Wani babban jigo a APC daga Arewa maso Yamma ya tabbatar da cewa za a yi ganawar tsakanin Tinubu da Kwankwaso a yau, idan shugaban ƙasa bai da abubuwa da yawa.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan haɗin kan siyasa da daidaiton ƙasa.
Wannan ya haifar da tambaya kan makomar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.
Duk da cewa magoya bayan Gwamna Abba na farin ciki da matakin sauya sheƙar, har yanzu ba a san ko Kwankwaso za bi su, su koma APC ba.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa duk wata haɗaka tsakanin Kwankwaso da APC za ta kawo gagarumin sauyi a siyasar Kano da Arewa baki ɗaya.
A wajen Tinubu, samun goyon bayan Kwankwaso da kuma gwamna mai ci zai ƙarfafa tasirin APC a Kano gabanin zaɓen 2027.
[ad_2]
Source link