Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 35 a Taraba

[ad_1]



Mahukunta a birnin Jalingo na Jihar Taraba sun tabbatar da mutuwar mutane 35 sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa.

Shugaban Sashen Kula da Lafiya na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Jalingo, Dokta Suleiman Abubakar Kirim, ya bayyana cewa an kwantar da marasa lafiya 226 da ake zargin sun kamu da cutar.

Bayan gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa mutum 95 daga cikinsu sun kamu da cutar, inda 35 suka rasu, yayin da 20 sun warke har an sallame su.

Ya kuma bayyana cewa ma’aikata uku na asibitin sun kamu da cutar da suka haɗa da likita da nas da direba wanda shi ya riga mu gidan gaskiya yayin da sauran biyun sun warke.

Dokta Kirim ya ce ƙididdigar waɗanda suka kamu da cutar da mace-macen da aka samu shi ne mafi girman alƙaluman da asibitin ya fitar a ‘yan kwanakin nan.

Ya gode wa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Taraba bisa goyon bayan da suke bayarwa.

Kazalika, ya shawarci jama’a da su riƙa kula da tsaftace muhalli matuƙa tare da hana ɓeraye masu yaɗa cutar shiga gidajensu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *