Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya

[ad_1]



Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124.

Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa suka kai kusan mutane biliyan 2.45 zuwa shekarar 2023.

Ƙasar Indonesia ce ke kan gaba da Musulmai miliyan 242, sai kuma Pakistan mai miliyan 235. Sai kuma ƙasar India da miliyan 213 sa’annan kuma Bangladesh da miliyan 150. Daga nan kuma sai Najeriya wacce ta biyo su da mutane miliyan 124.

Tarihi ya nuna cewa Musulunci ya fara shigowa Najeriya tun daga ƙarni na 11 ta hanyoyin kasuwanci na ‘trans-Sahara’ daga Arewaci da kuma Yammacin Afirka.

Sai kuma a ƙarni na 19, an kafa Daular Musulunci ta Sakkwato wacce ta ƙara jaddada addinin Musulunci musamman a yankin Arewacin ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *