DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu

[ad_1]



Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya (DSS) ta bai wa shafin sada zumunta na X wa’adin sa’o’i 24 da ya goge wani saƙo da mai fafatuka Omoyele Sowore ya wallafa yana ƙaryata Shugaba Bola Tinubu.

Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da Hukumar DSS ɗin ta aike wa kamfanin X Corp mallakin fitaccen attajirin nan Elon Musk.

A wasiƙar da DSS ta wallafa shafinta na X ranar Asabar, hukumar ta zargi Mista Sowore da yin amfani da saƙonsa na X wajen cin fuskar shugaban ƙasa Tinubu da yi masa rashin mutunci da ba’a.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar 25 ga watan Agusta, Mista Sowore ya soki ziyarar da shugaban Nijeriya ya kai Brazil da kuma kalaman da shugaban ya yi yayin ziyarar.

“Mai laifi @officialABAT (Bola Tinubu) ya kai ziyara Brazil inda ya ce babu cin hanci da rashawa a Nijeriya a gwamnatinsa. Ji wani ƙarfin hali na ƙarya da ko kunya babu!” in ji Omoyele Sowore (@YeleSowore) ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2025.

A cikin wasiƙar da DSS ta aike wa kamfanin X ta ce waɗannan kalaman sun ɓata wa magoya bayan Shugaba Tinubu rai, lamarin da ya sa suka yi zanga-zangar rashin amincewa da kalaman na Sowore a kan titunan ƙasar.

Saboda haka, hukumar ta bai wa shafin X wa’adin sa’o’i 24 domin ya cire kalaman Sowore ko kuma ta ɗauki matakai masu tsauri a kan shafin.

Abin da Tinubu ya ce a Brazil

Ana iya tuna cewa dai a yayin ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai ƙasar Brazil a watan jiya, ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi a Nijeriya sun kawo ƙarshen cin hanci a ƙasar.

“Sauyen-sauyen da na ƙaddamar tun da na karɓi ragamar mulki a Nijeriya suna tasiri sosai. Zan iya bugun ƙirji kan haka. Daga farko sun ba da wahala. Amma a yau sakamakonsu yana haɓaka,” in ji Shugaba Tinubu.

“Yana daɗa bayyana ga mutane. Mun ƙara yawan kuɗi cikin tattalin arzikinmu. Yanzu babu cin hanci da rashawa. Gwamnan babban bankin (Nijeriya) ya zo nan. Ba sai ka san shi ba kafin ka samu takardun kuɗin ƙasashen waje da kake buƙata,” in ji shi.

Martanin Sowore

Shi kuwa mai fafatuka, Omoyele Sowore, wanda hukumar DSS take ƙorafi game da saƙon da ya wallafa ya mayar da martani da saƙon DSS.

“Da safiyar yau, X (wanda a baya ake kira Twitter) ya tuntuɓe ni a hukumance game da wasiƙar barazana da suka samu daga hukumar DSS mara bin doka game da saƙon da na wallafa kan Tinubu. Ba zan goge saƙon ba,” in ji Sowore a saƙonsa na X.

Sai dai a halin yanzu abin jira a gani shi ne abin da zai biyo bayan wa’adin sa’o’i 24 da hukumar DSS ta bai wa X.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *