Siffofin Bahaushe A Shudadden Zamani Mai Nisa
[ad_1]
Idan ba a manta ba, a makonni biyu da suka gabata a wannan shafin, mun ga asalin Kalmar zamantakewa da yadda take a yanzu a kuma magance . Sannan mun ga ma’anar Kalmar zamantakewa, da iren-irenta, haka zalika, mun ga ina ake kira da kasar Hausa a yau? Da yadda tsarin zaman Hausawa yake kama ga bambanci ta fuskar rukuni ko matsayin a zuzuwan al’ummar Hausawa.
Bahaushe A Jiya
Idan aka ce jiya ta kasu gida biyu akwai jiya ta nesa da kuma jiya ta kusa . Jiya ta nesa ita ce Jiyan da Bahaushe yake zaune a matsayin maras addini saukakke daga Allah (S.W.A), sai dai addini irin na tsarin zaman ‘yar marina, wato kowa gabansa, ma’ana kowa yana bautar abin da ya ga ya cancanci ya bautawa. Amma a lokacin da addinin musulunci ya zo kasar Hausa da yawa daga cikin Hausawa suka rungume shi a matsayiin addini sabanin tsarin da suka taso suka tsinci kansu a ciki na bantar dodanni ko gumakansu.
- Binciken CGTN: Babban Layin Dogo Na Sin Da Turai Wani Sabon Kuzari Ne Ga Budadden Tattalin Arzikin Duniya
- Kasar Sin: Kashe Shugabanni Da Hare-Hare Kan Fararen Hula A Iran Abu Ne Da Ba Za A Lamunta Ba
Don haka, wadansu daga cikin su suka guji addinin Musulnci, da wannan ne wadancan bangare da suka karbi Musulunci suke kiran daya bangaren da suna maguzawa a matsayin jam’I amma a daidai ku Bamaguje, wato wanda ya guji addinin musulunci.
Amma idan muka ce nesa ta kusa ita ce, nesa da Bahaushe ya riga ya ya karbi addinin musulunci, ya zama riga a gare shi wato, al-adunsa da dabi’unsa mafi akasari sun rikide sun zama na Musulunci.
Don haka, a nan zamu kasa Hausawa da zamantakewarsu zuwa kashi uku, kamar haka:
Lokacin zama bai daya
Hausawa a zamanin Musulunci da maguzanci
Hausawa a zamanin Musulunci da zamantakewa da dai-dai kun Maguzawa.
Hausawa a lokacin zama bai daya. A wancan lokacin zamantakewar Hausawa, Ita ake kira da zamantakewa bai daya tare da Hausawan dauri. A lokacin mutane ne wadanda suka fahimci zamaninsu, sannan suka san kansu. Mutane ne da suka riki ababan bautarsu da gaskiya a wancan lokacin wanda tasirin hakan ya bayyana ta fuskar riko da addini a lokacin da Musulunci ya zo musu, sukai masa kyakkyawan riko. A wancan lokacin akwai wadansu abubuwa wadanda Hausawa suka rike, a cikin tsarin zamantakewarsu wadanda su suka saya wa Bahaushe girma da daukaka a tsakanin makwabtansu da sauran kabilu abokan zamansu.
Manufar rayuwa ga Bahaushen dauri ita ce a yi rayuwa ingantacciya cikin daraja da kaunar juna da kishin juna da taimakon juna. Bahaushe a wancan lokacin ya rike wadansu abubuwa muhimmai wadanda su ne gishirin zaman duniya wato a cikin abin da ya shafi al’amuran rayuwarsu.
Wadannan abubuwan su suka sa rayuwar Bahaushe a da ta yi inganci. Bahaushen jiya mai nisa yana da tattali da tsansteni da kulawa a al’amuransa na yau da kullum. Don haka ne ma yake da wani a zancin Magana da yake cewa kada-ran kada-han ma’ana kada-ka-ki-ci kada-ka cinye-duka, kuma komai zaka yi ka rinka sara-ka-na kallon bakin gatari. Bahaushe ya samu wannan falsafar ce domin shi kansa harshen Hausa a jiya mai nisa , harshe ne da yake cike da azanci da Karin Magana kuma azanci da karin Magana, suna daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen auna falsafar al’ummar duniya . Don haka za mu iya cewa, rayuwar Bahaushe a da cike take da falsafa wadda hakan ya kara taimaka masa cimma burace buracen rayuwa da ya sa a gaba.
Wadannan abubuwan suna daya daga cikin abubuwan da suka taka rawa wajen samun gida ko iyali na gari a cikin zamantakewar Bahaushe a zamanin dauri.
Siffofin Bahaushe A Zamanin Da Mai Nisa
Mutum ne mai takatsantsan kamar yadda muka ambata a baya, wannan taka tsantsan din nasa ya shiga cikin ko wane bangare na rayuwarsa kuma ga neman aure yakan yi tattali dan gudun kada ya shiga tsaka mai wuya hakazalika, yana da kulawa wajen harkar iyalinsa da aikinsa da sauran al’umuran yau da kullum. Wadansu daga cikin sifoffin da Bahaushen da ya siffantu da su sun hada: tsare gaskiya da amana a dukkan al’amuransa, da zumunci da kana’a ko dangana da hakuri game da halin da ya tsinci kansa ko ya tsinci kansa a halin rayuwa. Hakazalika, Bahaushe a da yana kiyaye dukkan wani abin da al’adarsa ta haramta masa ya aikata da kuma kawatawa cikin dukkan abin da al’adarsa ta halatta masa ya aikata, a takaice, za mu iya cewa, Bahaushe mutum ne mai kiyaye shari’a, sannan yana daga cikin siffofin Bahaushen da su ne, da’a ga manya ko jagorori a cikin al’umma.
Bahaushe mutum ne mai neman na kansa don haka nema yake da wata Karin Magana da take cewa a san mutum a san cinikinsa in ya bari a san ya daina. Don haka nema Bahaushe yake da sana’o’in gargajiya kamar noma da kiwo da fatauci da kira da saka da jima da dukanci da sasaka da kuma dori . A da ko ajiya musamman mai nisa za a tarar da Bahaushe kwarare ne a kan sana’arsa.
Wata fitacciyar siffa da aka san Bahaushen dauri yake da ita , ita ce jaruntaka . Bahaushen da jarumi ne kuma yana son jaruntaka, don haka ne ma yake zaune a sarari ba a cikin duhuwa ba, wanda hakan yana daga cikin siffa ta jarumin mutum don haka Bahaushe bai san lalaci ba, ko ragwanci ko kuma matuwar zuciya ba.
[ad_2]
Source link