Sin Ta Bukaci A Aiwatar Da Ra’ayin Kasancewar Bangarori Da Yawa A Duniya
A gabar da ake bikin cika shekaru 80 da kafuwar hukumar MDD mai lura da tattalin arziki da zamantakewar al’umma ko ECOSOC, kasar Sin ta bukaci a kara azamar aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya. Da yake tsokaci kan batun, yayin bikin murnar wannan lokaci a jiya Juma’a, jami’in gudanarwa, kuma mukaddashin jakadan Sin a MDD Sun Lei, ya jaddada muhimmancin aiwatar da hakan.
Sun Lei, ya ce a halin yanzu, duniya na fama da rigingimu da tangal-tangal, don haka ya wajaba hukumar ta ECOSOC ta sauke nauyin dake wuyanta a tarihi, tare da cimma nasarar muhimman ayyuka uku. Wato da farko, ta ingiza ruhin ainihi na kafuwarta, da aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya.
Na biyu kuma, ta fifita samar da ci gaba da karfafa hadin gwiwa. Kana na uku ta yi tafiya kafada-da-kafada da zamanin yau, da kyautata tsarin jagorancin kasa da kasa.
Sun Lei, ya kara da cewa, karkashin tanadin shawarar nan ta bunkasa jagorancin duniya ko GGI, kasar Sin ta samar da kudade har sama da dalar Amurka biliyan 23, ta kuma aiwatar da ayyukan hadin gwiwa sama da 1,800, tare da yin ayyuka na zahiri, don taimakawa kasashe masu tasowa su cimma ajandarsu ta nan zuwa shekarar 2030.
Kazalika, Sin na aiki tukuru tare da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, wajen yayata goyon baya ga hukumar ECOSOC, ta yadda za ta kai ga cimma manyan nasarori a fannin bunkasa ci gaba tsakanin dukkanin kasashen duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)