Gwamnatin Kano ta gargaɗi magoya bayanta kan cin mutuncin Kwankwaso

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kano, ta gargaɗi magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da su guji yin kalaman ɓatanci ko cin mutuncin jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamnatin ta ce duk wanda ya raina ko ya zagi Kwankwaso zai fuskanci hukunci.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya yi wannan gargaɗi a ranar Asabar.

Ya bayyana haka ne yayin rabon babura ga ’yan jam’iyyar aFadar Gwamnatin Kano.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya halarci taron.

Bature, ya ce gwamnati ba za ta lamunci rashin ladabi ko rashin girmama Kwankwaso ba, inda ya bayyana shi a matsayin jagora da ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Kano.

“Ba za mu yadda da rashin ɗa’a ko zagin jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ba. Duk wanda ya aikata hakan zai fuskanci hukunci. Ba za mu amince da hakan ba,” in ji shi.

Ya shawarci magoya bayan gwamnan da su kasance masu natsuwa da biyayya, musamman a wannan lokaci da aka samu sauye-sauyen siyasa a jihar.

A cewarsa, gwamnati na da ƙudirin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin magoya bayanta, yana mai jaddada cewa saɓanin siyasa bai kamata ya rikiɗe zuwa zagi ko cin mutunci ba.

Bature ya kuma tunatar da magoya bayansu cewa girmama shugabanni da yin ladabi a tsarin siyasa na da matuƙar muhimmanci wajen samun zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci.

Wannan gargaɗi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara bayan murabus ɗin Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *