’Yan majalisar dokokin Kano 22 sun fice daga jam’iyyar NNPP

[ad_1]



Aƙalla ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano 22 ne, suka fice daga jam’iyyar NNPP, domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, an ce ’yan majalisar sun ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da biyayyarsu ga gwamnan, biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

An bayyana cewa hakan na da nufin ƙarfafa matsayinsa a siyasa.

Daga cikin waɗanda suka fice akwai Kakakin Majalisar, Mataimakin Kakakin Majalisar, Shugaban Masu Rin­jaye na Majalisar da sauran ’yan majalisa daga mazaɓu daban-daban.

’Yan majalisar sun ce sun amince da matakin da gwamnan ya ɗauka na fucewa daga NNPP, kuma suna jiran mataki na gaba da zai ɗauka game da jam’iyyar da za su koma.

Ko da yake Gwamna Abba Kabir Yusuf bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a hukumance, alamu na nuna cewa yana dab da komawa jam’iyyar APC.

Da wannan sauyin, ana sa ran Majalisar Dokokin Kano mai mambobi 40 za ta koma ƙarƙashin ikon jam’iyyar APC, lamarin da ka iya sauya tsarin siyasar jihar a nan gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *