Tawaga Ta 26 Ta Jami’an Kiwon Lafiyar Sin Ta Isa Rwanda
[ad_1]
An gudanar da bikin maraba da zuwan tawaga ta 26, ta jami’an kiwon lafiya na kasar Sin da za su yi aiki a kasar Rwanda, yayin da tawagar da ta kammala aiki ke ban kwana da kasar.
An gudanar da bikin ne a birnin Kigali fadar mulkin kasar, wanda hakan ya shaida karin dankon hadin gwiwar sassan biyu a fannin kiwon lafiyar jama’a. Yayin bikin na daren ranar Alhamis, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta kasar Rwanda Ndayizigiye Jean Marie Vianney, ya jinjinawa jami’an lafiya na kasar Sin, bisa jajircewarsu wajen gudanar da aiki cikin himma. Yana mai cewa “A asibiti, ko kananan cibiyoyin kula da marasa lafiya, ko unguwanni, kuna ayyuka bisa juriya, da kwarewa da sadaukarwa. Muna sane da kokarin da kuke nunawa.”
Babban sakataren ya kara da cewa, gudummawar jami’an lafiyar ta shaida tagomashi, da bunkasar kyakkyawar alakar dake akwai tsakanin Rwanda da kasar China, musamman a fannin kiwon lafiya, yayin da cudanyarsu ta haifar da musayar kwarewa da ilimi, da tasiri mai wanzuwa.
A nasa tsokaci kuwa, shugaban tawaga ta 25 ta jami’an lafiyar kasar Sin Wang Yongxiang, cewa ya yi cikin kusan shekara guda da ta shude, jami’an lafiya na Sin, sun taimaka wajen gina tsarin aikin kwararru a fannin aikin kashi, da cibiyar jinya mai cikakken tsarin kawar da radadi a asibitin Kibungo, sun kuma gabatar da fasahohin kasar Sin irinsu na tsira allurai domin magani, da haihuwa marar radadi, da shawo kan yaduwar cututtuka masu bazuwa ga likitocin kasar, wanda hakan ya haifar da alfanu mai dorewa ga tsarin kiwon lafiyar kasar, da jama’ar kasar ta Rwanda. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link