Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

[ad_1]


Birigediya Janar M. Uba, Kwamandan Rundunar Sojin Nijeriya ta 25, ya rasu bayan Boko Haram/ISWAP sun yi kai harin kwantan-ɓauna a Wajiroko, ƙaramar hukumar Damboa a Jihar Borno.

Tun da farko, sojoji sun tabbatar da mutuwar sojoji biyu da CJTF biyu, amma suka ƙaryata rahotannin kashe Kwamandan Rundunar.

Majiyoyi sun ce an kai ruwa rana da Janar Uba yayin  arangamar, kafin daga baya ’yan ta’addan suka kama shi yayin da yake ƙoƙarin komawa sansani.

Duk da cewa rundunar soji ta yi zaton ya tsira, ’yan ta’addan sun tabbatar da cafke.

Ƙungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta ti iƙirarin kashe Janar Uba.

“Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.”

An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure.

Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *