Kafar Yada Labarai Ta Afirka Ta Kudu: Matakan Soke Haraji Na Sin Sun Karfafa Kokarin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Gina Zamanantarwa
[ad_1]
A ranar 17 ga watan nan, shafin yada labarai na Independent Online (IOL) da ke kasar Afirka ta Kudu ya wallafa makalar David Monyae, darektan cibiyar bincike ta Afirka da Sin ta jami’ar Johannesburg, wadda a ciki ya bayyana cewa, shirin soke harajin kayayyaki na kasar Sin ga kasashen Afirka 53 da suke da alakar diflomasiyya, zai kawo sabbin damammaki ga bangarorin biyu wajen gina zamanantarwa cikin hadin gwiwa. Ya kamata kasashen Afirka su kara karfin kansu, su yi amfani da damar da suka samu, sannan su mayar da hangen nesansu zuwa ga samun nasara a aikace.
Makalar ta yi nuni da cewa, a daidai lokacin da duniya ke bukatar hadin gwiwa ta hakika fiye da kowane lokaci, Sin da Afirka na kulla huldar kasuwanci ta kud-da-kud. Kasar Sin na neman samun ci gaba na bai-daya ta hanyar hadin gwiwa da kasashe masu tasowa. Kasar Sin ta sanar da cewa, za ta aiwatar da cikakken shirin soke haraji ga kayayyakin kasashen Afirka 53 masu alakar diflomasiyya da ita daga ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2026. Manoman Afirka, masu masana’antu, da masu hakar ma’adanai za su iya sayar da kayayyakinsu cikin sauki, ta yadda za su kara samun kudaden shiga da kuma damammakin ayyukan yi.
Makalar ta jaddada cewa, cinikayyar Sin da Afirka na samar da moriyar juna da nasara ga ko wane bangare. Mikewar Afirka ba aba ce da za ta yi a cikin kadaici ba, a’a, ci gaba ne na hadin gwiwa tare da kasashe kawayenta irin kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link