APC Ga Atiku: Dimokuraɗiyyar Nijeriya Ba Ta Cikin Barazana
[ad_1]
Jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar cewa, dimokuraɗiyyar Nijeriya na fuskantar barazana, tana mai bayyana zargin a matsayin abin takaici da ban dariya.
Atiku, ta bakin mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da raunana jam’iyyun adawa da gangan da kuma yunƙurin tauye dimokuraɗiyyar Nijeriya, yana mai gargadin cewa, ana shirin mayar da ƙasar tsarin jam’iyya ɗaya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Biya ‘Yan Wasan Super Eagles Haƙƙoƙinsu
- Wang Yi Zai Ziyarci Habasha Da Somalia Da Tanzaniya Da Lesotho
Ya kuma yi zargin cewa, ‘yan Nijeriya sun fuskanci kusan shekaru uku na matsanancin matsin tattalin arziki a karkashin gwamnatin Tinubu, tare da manufofin da ke karya tanadin dimokuradiyya.
Amma, da yake mayar da martani a ranar Alhamis, kakakin jam’iyyar APC reshen jihar Legas, Seye Oladejo, ya ce Atiku da ƙawancen jam’iyyarsa ta ADC, kawai suna “tsoron ranar da za su sha kaye ne.”
Oladejo ya nace cewa, cibiyoyin dimokuraɗiyya suna aiki yadda ya kamata a karkashin Shugaba Bola Tinubu, yana mai kira ga ‘yan adawa da su daina neman mafaka tun yanzu, gabanin ranar da za su sha kaye.
[ad_2]
Source link