Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Dungurawa A Kano

[ad_1]

Kwamitin gudanarwa na Kasa (NWC) na Jam’iyyar NNPP, ya ayyana dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, a matsayin hukuncin da ba shi da tushe kuma an jefar da hukuncin.

NWC ta zargi matakin da wasu shugabannin jam’iyyar suka dauka a ‘Gargari Ward’, karamar hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano, wadanda suka sanar da dakatarwar da suka yi wa Dungurawa, a matsayin wani babban aikin cin amanar jam’iyya wanda matakin na su ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar NNPP na Kasa, Bamofin Ladipo Johnson, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce NWC na jam’iyyar ta sake tabbatar da matsayin Dungurawa a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar NNPP a Jihar Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *