Ko Za A Yankani Ba Zan Koma APC Ba – Gwamnan Bauchi
[ad_1]
Daga Khalid Idris Doya
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa wajen musguna wa ‘yan adawa da ci musu mutunci, ya bayyana cewar saboda ya ƙi ya koma cikin APC ne ta masa bi ta da ƙulli.
Gwamnan ya yi zargin ne bayan sanya hannu kan kasafin kuɗin jihar na 2026 a ranar Laraba, inda ya nuna cewa ko da yankashi za a yi ba zai taɓa komawa APC ba.
- GGI Da Kasar Sin Ta Gabatar Ta Samar Da Mafita Ga Kasashen Da Ke Cikin Mawuyacin Hali
- Saƙon Sakatare Janar Na MDD, Antonio Guterres Na Shiga Sabuwar Skekarar 2026
Idan za a tuna dai EFCC ta cafke Kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi Yakubu Adamu da farko an zargi da hannu wajen almundahana da sama da Naira biliyan 5, sai kuma a ranar Laraba hukumar ta sake gurfanar da shi bisa sabon zargin da hannu a taimaka wa ayyukan ta’addanci ta hanyar tallafawa da kuɗaɗe.
Gwamnan jihar Bauchi ya ce wasu gwamnoni sun koma APC bisa wasu dalilai, amma shi saboda ya ƙi komawa cikin APC ne ya sanya gwamamtin tarayya ke musguna masa.
“Wasu ‘yan uwa gwamnoni sun bar ni sun koma APC bisa waɗansu dalilai ni kuma na ƙi, sai ana ci min mutunci, ana cin mutunci ma’aikatana, ana cin mutunci iyalaina ana so a mana ƙazafi har ma da cewa muna cikin masu kawo harkokin ta’addanci; wanda babu ta’addanci a Bauchi, zaman lafiya ake yi.
“Kuma aka kawo sunan wani wai Bodejo wanda ƙanine a wajena kuma ba a nan garin ya ke ba, a Nasasawa ya ke. Kuma ba ni ya fara taimaka a siyasa ba; ya taimaki mai girma shugaban ƙasa, ya taimaki gwamnan Nasarawa, in ya na da matsala ba kawai za a haɗashi da shi da ni kawai don shi Bafulatani ba ne.
“Ni na riga na faɗa a baya. Duk wanda ya ci mutuncin Bafulatani saboda banbancin yare ba zan bar shi ba. Saboda haka na kare Badejo saboda na san ban taɓa ganinsa da ta’addanci ba.”
Gwamnan ya ce saboda kawai ana son a ɓata shi ne aka haɗashi da Bello Badejo saboda hasashen siyasa, ya nuna hakan da cewa ba daidai ba ne.
“An ɗauki kwamishina na an rufe shi an masa ƙazafofi iri-iri. Kuma a matsayina na gwamna ina da kariya na musamman bai kamata ake sanya sunana a cikin kotu ba. Ko wani abu na yi na kisa ma sai na sauƙa. Amma saboda ba su san gwamnati ba kuma gwamnatinsu na cin mutunci abun da suke yi kenan.
“Na yi shiru saboda ba na son mu yi maganganun da za su kawo fararraƙa ƙasa tun da ƙasar ma a ɓare ta ke. Ga talauci, ga yaudara, ga ƙarya, ga yunwa amma kullum ana ƙarya wa mutane. Ana karɓar bashi ba a san me ake yi da shi ba. Ana karɓar kashi 51 na kuɗin Nijeriya ba a san me ake yi da shi ba,” ya yi zargi.
Ya ƙara da cewa su kuɗaɗen da suke samu a jihohi suna aiki da su, sai ya yi zargin cewa wasu gwamnonin ba su aiki da kuɗaɗen da suke samu amma su ba a taɓa su.
“Sai mu da muke aikin ake taɓawa saboda ana duba kila a gaba za mu zama wani abu; zama wani abu ai na Allah ne.”
Ya ce adawa dole ne kuma babu wanda ya isa a tursasa masa fita a PDP domin ya koma APC, “Ko za su yankani ina inda na ke ni da mutanena. Mutanen Bauchi sun ce kar na je ko’ina.”
[ad_2]
Source link