Tinubu Ya Rantsar Da Taiwo Oyedele A Matsayin Ƙaramin Ministan Kuɗi

[ad_1]

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin Karamin Ministan Kudi a ranar Litinin a Abuja.

Oyedele, wanda ya taɓa zama shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan sauye-sauyen haraji, ya karbi rantsuwar ne bayan naɗa shi a wannan muƙami. Ya maye gurbin Doris Uzoka-Anite, wacce aka mayar da ita Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi.

  • Mun Ceto Nijeriya Yayin Da Take Gab Da Dilmiyewa – Tinubu
  • Tinubu Da Shettima Sun Yi Buɗa-Baki Da Sarakuna Da Malaman Addini A Villa

A baya dai shugaban ƙasa Tinubu ya aikewa da majalisar dattawa sunan Oyedele domin tantancewa da tabbatar da naɗin nasa, bayan majalisar dokoki ta amince da wasu dokokin gyaran tsarin haraji da kwamitinsa ya jagoranta.

Taiwo Oyedele, ɗan asalin garin Ikaram-Akoko a Jihar Ondo State, masanin tattalin arziƙi ne mai shekaru 50 da ƙwarewa a fannin kuɗi, da haraji da manufofin tattalin arziƙi. Ya fara karatunsa a Yaba College of Technology inda ya samu HND a fannin lissafi da kuɗi, sannan daga baya ya samu digiri a Applied Accounting daga Oxford Brookes University a United Kingdom.

Kafin shiga aikin gwamnati, Oyedele ya shafe shekaru 22 yana aiki da kamfanin PricewaterhouseCoopers inda ya fara aiki a 2001 har ya zama jagoran harkokin haraji na Afirka. Haka kuma yana koyarwa a Babcock University a Jihar Ogun State, sannan yana matsayin baƙo mai bincike a Lagos Business School.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *