Sauya sheƙar Abba ba a Kano ta tsaya ba

[ad_1]



Duk da roƙon da jagoran Jam’iyyar NNPP na ƙasa kuma Madugun tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sake tunani kan shirin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC, manyan makusantan gwamnan sun ce gwamnan ya riga ya yanke hukunci kuma ba zai sauya ba.

Wani na kusa da gwamnan ya shaida wa wakilinmu cewa sauya shekar ba batun Kano ba ne, batun Fadar Shugaban Ƙasa ne.

Tun makon jiya maganar sauya sheƙar ta mamaye tattaunawar siyasa a Kano, inda ake raɗe-raɗi cewa za a sanar da shi a ranar 5 ga Janairu.

Sai dai majiyoyinmu sun ce ba a kafa wata rana ba tukuna, saboda gwamnan na ci gaba da tuntuɓa don kauce wa rikice-rikice ko ruɗani a harkokin mulki.

Rahotanni sun nuna cewa an fara shirin yi masa rajista a Hedikwatar APC ta Ƙasa da ke Abuja, a matsayin mai riƙe da Lamba ta ɗaya a Kano, ƙarƙashin sabon tsarin rajistar mambobin jam’iyyar ta intanet.

Amma sun ce an dakatar da shirin bayan an ba shi shawarar ya fara ganawa da manyan jagororin APC a Jihar Kano, musamman tsohon gwamna kuma tsohon shugaban jam’iyya na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.

Sai dai wani na kusa da gwamnan ya ce duk wannan magana jita-jita ce: “Ba mu taɓa sanya rana ba. An riga an kammala yanke hukunci kuma za a sanar da ranar idan aka gama shirya komai. Masu cewa yau (Litinin) za a yi, suna yada jita-jita ne kawai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sauya sheƙar, bai dogara da sharaɗin tuntuɓar shugabannin APC na Kano ba.

“Batun Fadar Shugaban Ƙasa ne, ba batun Kano ba. Wannan magana tsakanin gwamna da shugaban ƙasa ce, ko kuma shugabannin jam’iyya na ƙasa da aka ɗora wa alhakin shirin,” in ji shi.

Sai dai ya ce gwamnan na ci gaba da tuntuɓa a matsayin ɗan dimokuraɗiyya don ya ja ragamar magoya bayansa daga NNPP tare da kauce wa rikici a cikin APC a Kano.

Ainihin dalilan sauya sheƙar Abba

Majiyar ta ce hukuncin gwamnan ya ta’allaƙa ne da ci gaban mulki da walwalar Kano, ba wai son zuciya ba buƙatun ƙashin kansa kawai.

“NNPP ba ta da ƙarfi a yanzu. Jam’iyyar ta koma a takarda kawai. Babban dalilin gwamna shi ne ya sa Kano matsayin da za ta fi amfana daga Gwamnatin Tarayya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa akwai manyan ayyuka da dama a jihar, kuma suna buƙatar tallafin Gwamnatin Tarayya.

A cewarsa, “Kano ce jiha da ta fi yawan jama’a a Najeriya, da sama da mutane miliyan 22. Duk da kasafin jihar na Naira tiriliyan 1.47, amma  ba za ta iya ɗaukar nauyin manyan ayyuka ita kaɗai ba,” in ji shi.

Ya kawo misalin aikin Wujuwuju da aka fara a zamanin mulkin Kwankwaso, wanda ya ce kuɗin aikin ya ƙaru Naira biliyan 47, kuma yanzu yana buƙatar sama da Naira biliyan 100 kafin ya kammala.

Haka kuma ya nuna damuwa kan matsalar tsaro.

“Matsalar ’yan bindiga babban ƙalubale ne. Dole ne a samu haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro na tarayya.”

Ya ƙara da cewa rikicin cikin gida na NNPP da kuma tsamin dangantaka tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso na daga cikin abubuwan da suka sa gwamnan ya ƙara tabbatar da hukuncin.

“Duk waɗannan dalilai ne suka sa gwamna ya ɗauki wannan mataki. Hukuncin ba zai sauya ba, duk da matsin lamba daga tsohon ubangidansa na siyasa, Kwankwaso, wanda tuni ya riga ya yanke cewa ba zai bari gwamna ya samu wa’adi na biyu ba,” in ji majiyar.

Martanin Kwankwaso

A makon da ya gabata, majiyoyi sun tabbatar da cewa Gwamna Abba na iya sauya sheƙa zuwa APC ko da ba tare da yardar Kwankwaso ba, lamari ya haifar da savani tsakanin tsoffin abokan siyasar.

Rikicin tsakanin ya riga ya bayyana, kuma majiyoyi sun ce, shugabannin biyu sun riga an ja layi a tsakaninsu, kuma idan ba a samu sulhu ba, shugabannin biyu na iya fara sukar juna a fili.

A ƙarshen mako, Kwankwaso ya tabbatar da wannan saɓani yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Kano.

Ya bayyana a fili cewa ba ya goyi bayan sauya shekar ba, da cewa, “Ba na cikin wannan shiri, kuma ba na goyon bayan sauya sheƙa daga jam’iyya. Dole ne kowa ya sani.”

Kwankwaso ya ƙara da cewa, “Abu mafi ciwo shi ne a ɗauke nasarar zaɓe da wahala zuwa wurin abokan adawa, musamman na tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.”

Ya zargi wasu da ya ce su ne ke ƙoƙarin tursasa sauya shekar, yana mai cewa ya kamata su ba wa gwamnan shawarar gwamnan ya ajiye kujerarsa  kafin ya koma APC.

Alaƙar Kwankwaso da Abba

Kwankwaso ya tuna yadda shi kaɗai ya zaɓi Yusuf a matsayin ɗan takarar gwamna na Kwankwasiyya a 2019 karkashin PDP, wanda ya sha kaye a zaben.

A 2023 kuma, tare da goyon bayansa, Abba ya lashe zaɓen gwamna bayan ya doke ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki da Ganduje ya ɗora.

Ya roƙi magoya bayansa da su ci gaba da addu’a da kuma lallashin gwamnan ya janye batun sauya sheƙa.

“Ba ma son su tafi. Muna son su zauna. Amma idan suka nace, rayuwa za ta ci gaba,” in ji shi.

Kwankwaso ya bayyana cewa APC da Gwamnatin Tarayya sun tuntube shi, amma tayin da suka yi masa da kuma hujjojinsu ba su da ƙarfi.

“Mun zauna muka tsara tsare-tsare masu kyau, amma wannan tafiya ba ta ta’allaka da ni kaɗai ba. Na tambaye su abin da za su mu, ni da shugaban jam’iyya da shugabanni da magoya baya, amma ba su da amsar da ta gamsar da ni,” in ji shi.

Ya ce tafiyar NNPP ba ta da rauni kamar yadda ake iƙirari, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na da tsari a duk faɗin ƙasar nan kuma har yanzu ita ce babbar jam’iyya a Kano.

Yiwuwa sauya sheƙar Kwankwaso

Sai dai Kwankwaso bai kore yiwuwar shigarsa wata jam’iyya ba, muddin aka tabbatar masa da tikitin shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa.

Wannan ya ƙara ƙarfafa rahoton da ya nuna ana shirin haɗa shi da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar Labour a 2023, Peter Obi, a matsayin tikitin haɗin gwiwa don ƙalubalantar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a karkashin inuwar Jam’iyyar ADC.

Majiyoyi sun ce Kwankwaso ya amince da shirin ne bayan ganawarsa da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, wanda ya lallashe shi ya karɓi matsayin mataimakin shugaban ƙasa tare da Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Idan abubuwan suka tafi a haka ba a samu sauyi ba, ana sa ran Kwankwaso zai sauya sheka zuwa ADC a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɗa ’yan adawa gabanin zaɓen 2027 domin ƙalubalantar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu mai ci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *