Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa ga matar da ta kashe tsohon mijinta
[ad_1]
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Sakkwato ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Jihar Kebbi ta yanke wa wata mata mai suna Farida Abubakar, bisa laifin kisan tsohon mijinta, Babban Alkalin Kotun Majistire, Attahiru Muhammad-Ibrahim.
A watan Yuni, 2024, Babbar Kotun Birnin Kebbi ta yanke wa Farida hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same ta da laifin kisan kai mai ɗauke da hukuncin kisa.
Amma Farida ta garzaya Kotun Ɗaukaka Kara ta Sakkwatoo don ƙalubalantar hukuncin.
Sai dai kwamitin alkalan kotun mai mutum uku, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Tunde Oyebamiji Awotoye, ya yi watsi da ɗaukaka karar Farida, ya kuma tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke.
Mai Shari’a Awotoye ya ce, “Daukaka ƙarar ba ta da hujja. Don haka, wannan kotun ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Kebbi ta yanke a ranar 03/06/2024.”
A lokacin shari’ar farko, masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Barista Zainab Muhammad Jabbo daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kebbi sun kira shaidu 12 tare da gabatar da hujjoji da dama, ciki har da bayanin da Farida ta bayar a wajen ’yan sanda.
Sai dai lauyanta, Barista A. N. Salau, ya yi jayayya cewa kotun ta yi kuskure wajen yanke hukunci bisa hujjoji da ba su da ƙarfi.
Amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da hujjar lauyan, tana mai cewa shaidun da aka gabatar “sun suna da ƙarfi kuma ba a musanta su ba,” don haka sun wadatar wajen tabbatar da laifin fiye da shakku.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link