An Kama Mutane 3 Kan Ƙone Gidan Wata Mata A Kwara
[ad_1]
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta kama mutane uku bisa zargin ƙone gidan wata mai bin addinin gargajiya a unguwar Isale Koko da ke Ilorin.
Matar, Misis T. A. Olorisha, ta kai rahoto cewa an ƙone mata gida a ranar 1 ga watan Janairu, 2026, a lokacin da ba ta nan.
- AFCON 2025: Super Eagles Sun Murƙushe Mozambique Da Ci 4–0
- Za A Biya Super Eagles Kyautar Miliyan 14.5 Kan Kowace Ƙwallon Da Suka Ci A Wasa Da Mozambique
Ta ce tun a watan Nuwamban 2025 take fuskantar barazana saboda bambancin addini.
‘Yan sanda sun tabbatar da kama mutanen kuma sun ce suna ci gaba da bincike a kan lamarin.
Ba a samu asarar rai ba, amma har yanzu ba a tantance adadin asarar dukiyar da gobarar ta jawo ba.
Hukumomi sun ce suna ƙoƙarin kamo sauran waɗanda ke da hannu tare da tabbatar wa jama’a cewa an ɗauki matakan kare lafiyarsu.
[ad_2]
Source link