Sin Ta Baiwa Kauyen Gwaji Na Rage Talauci Na Sin Da Habasha Na’urorin Aikin Noma
[ad_1]
Kungiyar manyan kwararrun masana noma na Sin mai bayar da taimako a Habasha zagaye na 4, sun ba da na’urorin aikin noma ga kauyen nune-nune na farko na rage talauci ta hanyar noma na Sin da Habasha, wato kauyen Godino a yankin Oromia kyauta, don taimakawa harkar noman gida.
Bisa taimakon wurin, membobin kungiyar kwararrun masana noma ta Sin, sun sanya na’urorin shuka masara, da famfunan ruwa, da fitilun kashe kwari sama da 70 a cikin wasu manyan motoci, sun isar da su kauyen Godinoda da sassafe ranar Laraba 26 ga watan nan na Nuwamba.
Shugaban kungiyar manyan kwararrun masana noma ta kasar Sin Zhang Shihong ya bayyana cewa, kungiyar tana da mambobi 8, kuma sun isa Habasha a watan Agustan shekarar 2024 don aiwatar da aikin agaji. An kaddamar da aikin kauyen gwaji na rage talauci ta hanyar noma na Sin da Habasha ne a karshen watan Mayun bana, kuma yana da mahimmanci ga manyan kwararrun masana noma na zagaye na hudu na Sin a Habasha, da burin rage talauci a wurin ta hanyar amfani da gogewar Sin, tare da la’akari da yanayin Habasha, ta hanyar ba da iri, da dabbobin kiwo, da kayayyakin noma, da yada fasahar noma mai yawan yabanya, da kiwon lafiyar dabobbi, da ban ruwa bisa salon tsuminsa, don taimakawa manoman yankin su rage talauci, da cimma ci gaba mai dorewa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link