Adadin wadanda aka kashe a harin masallaci a Katsina yanzu ya kai 32
[ad_1]
Gwamnatin jihar Katsina ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da ’yan bindiga suka kai kan masallata a kauyen Unguwar Mantau na karamar hukumar Malumfashi, a yanzu ya karu zuwa 32.
Da sanyin safiyar Talata ne maharan suka bude wa mazauna kauyen wuta lokacin da suke gabatar da sallar Asuba a masallaci, inda a nan take aka tabbatar da mutuwar mutum 13 da jikkata wasu da dama.
To said ai ya zuwa yammacin Laraba, gwamnatin jihar, yayin wata ziyarar ta’aziyya da tawagarta ta kai yankin, ta tabbatar da karuwar adadin.
A cikin wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ya fitar, ta ce Gwamnan jihar, Dikko Radda ne ya tuntubi Mataimakinsa kan bukatar tura tawaga mai karfi domin jajantawa kasancewar yanzu haka ya tafi hutun neman lafiya kasar waje.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari ne dai ya jagoranci tawagar wacce Hakimin yankin ya karbe ta.
Faskari yayin ta’aziyyar ya bayyana harin a matsayin abin takaici kuma mai ratsa zuciya.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba a yunkurin da take yi na inganta tsaro da dawo da zaman lafiya a jihar.
Tawagar ta kuma shaida wa wadanda harin ya shafa cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta tallafa musu da kayan agaji.
Daga cikin ’yan tawagar jajen akwai Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida, Dr Nasir Mu’azu da mataimaka da masu ba gwamna shawara da dana majalisar jiha na Malumfashi da Ciyaman din karamar hukumar da kuma shugabannin hukumomin tsaro da ke jihar, ciki har da Kwamishinan ’yan sandan jihar.
Aminiya ta gano cewa harin na ramuwar gayya ne biyo bayan wanda mazauna yankin suka kai kan ’yan ta’addan, wanda ya kai ga kashe da dama daga cikinsu sannan aka kwace musu makamai da babura.
Wani mazaunin yankin da bai amince a bayyana sunansa ba ya ce ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai iya haura na farkon kasancewar an garzaya da wasu da suka samu raunuka zuwa asibiti a cikin mummunan yanayi.
Galibi dai a kan samu karuwar hare-haren ’yan ta’adda a yankuna da dama na jihar ta Katsina, musamman da damina lokacin da manoma suke aikin gona.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link