Majalisa za ta yi dokar kula da harkar Crypto da POS
[ad_1]
Majalisar Wakilai ta fara yunkurin kafa dokar da za ta daidaita harkokin kudin zamani na Crypto da kuma harkokin POS a Najeriya.
Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce yin hakan ya zama dole saboda yadda damuwa ke karuwa kan zamba, laifukan intanet, daukar nauyin ta’addanci da cin zarafin masu amfani da irin wadannan hanyoyin kudi.
Ya ce, “Akwai damuwa ta gaskiya kan yadda ake iya amfani da kudin zamani wajen daukar nauyin ta’addanci da safarar kudaden haram, la’akari da yadda tsarin yake da duhu, dole a yi tsayayyiyar doka doka ba, da kuma cikakken binciken yadda ake sarrafa kudaden.”
Abba ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani kwamitin wucin gadi a ranar Litinin domin nazarin tasirin tattalin arziki, dokoki da tsaro da ke tattare da mu’amalar kudi ta zamani.
Ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya nuna jajircewa sosai a cikin shekaru, inda ya farfado daga durkushewa kuma ya samu ci-gaba a sassan da ba na mai ba.
A cewarsa, hakan ya nuna cewa akwai yanayi da ya dace da cinikayyar kudin zamani. Sai dai ya gargadi cewa akwai manyan gibi da bai kamata a yi sakaci da su ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link