Babban layin wutar lantarki ya sake faɗuwa
[ad_1]
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa.
Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa.
Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba.
Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa.
Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe.
“Saƙonmu zuwa gare ku shi ne, rashin wutar da ake fuskanta yanzu ya faru ne saboda matsalar da ta samu daga layin ƙasa.
“Wannan ya shafi yankunan da muke bai wa wuta. Muna aiki tare da hukumomin da suka dace domin a dawo da wuta da zarar an komai ya daidaita. Mun gode da haƙurinku,” in ji AEDC.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link