Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
[ad_1]
Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne.
Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar Katutu, wacce ta haɗa ƙananan hukumomin Shinkafi da Isa.
Guyawa, ya bayyana cewa Turji tafe da maharansa a kan babura 40.
Haka kuma ya zargi hukumomin yankin da jami’an tsaro da rashin ɗaukar mataki duk da samun wannan bayanai.
Amma Shugaban Ƙaramar Hukumar Isa, Alhaji Sharehu Abubakar Kamarawa, ya ƙaryata zargin.
Ya ce tun bayan samun bayanin, suka tura jami’an tsaro domin ɗaukar matakin.
“An tura jami’an tsaro zuwa wajen da aka samu labari, amma daga baya bayanan sirri suka nuna cewa ‘yan bindigar sun bi wata sabuwar hanya, abin da ya haifar da wannan mummunan hari,” in ji Kamarawa.
Ya ƙara da cewa an sauya kwamandan tsaron yankin bayan binciken da aka gudanar tare da gano matsaloli wajen tsara aikinsa.
Kamarawa, ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar cewa gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Hakazalika, ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu bisa ƙoƙarinsa na yaƙi da ta’addanci, musamman ta hanyar raba motocin sintiri da babura ga jami’an tsaro ba su alawus na wata-wata.
Duk da waɗannan ƙoƙari, matsalar rashin tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan Jihar Sakkwato, musamman yankin gabas, inda ’yan bindiga ke ci gaba kai wa yankunan karkara hare-hare.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link