Yadda Ake Inganta Tsarin Harkokin Kudi Na Dattawa A Kasar Sin
[ad_1]
Sin a matsayin kasa mai tafiya a kan turbar fifita rayuwar al’umma, tana kara mai da hankali kan inganta tsarin yadda dattawa za su rika tafiyar da sha’anin kudadensu, yayin da take kara kimtsa wa karuwar adadin mutanen da ke tsufa. Bisa yadda take da adadin fiye da mutane miliyan 310 masu shekaru 60 zuwa sama, da kuma fiye da miliyan 45 masu bukata ta musamman, kasar ta himmatu wajen inganta tsarin kudi mai nagarta ga dattawa.
A duk fadin kasar, larduna da biranen suna fitar da sabbin tsare-tsare don inganta harkokin kudi su zama masu sauki ga dattawa. Misali, lardin Guangdong ya bullo da matakai 15 don gina wani tsarin hada-hadar kudi na dattawa a lardin nan da shekarar 2028. Manufar hakan ita ce samar da ingantacciyar hanyar zuba kudade a cikin asusun fansho da kuma kyautata muhimman ayyukan kula da dattawa.
Sauran yankuna kamar Jilin, Chongqing, da Qingdao su ma suna kara mayar da hankali kan wannan, inda Qingdao ta kaddamar da wani shiri na shekaru uku wanda ke sada ayyukan hidimomi na kudi da inshorar kiwon lafiya, da harkokin jama’a, da kuma kula da dattawa. Jilin kuma tana karfafa gwiwar masu gudanar da al’amuran inshora wajen ganin sun fadada nau’o’in ayyukansa da kuma habaka ba da kariya ga kudaden dattawa.
Wadannan matakai da yankunan kasar Sin ke daukawa sun zo a kan gaba, musamman bisa karuwar yawan dattawa kuma duk da yawancin dattawan yanzu suna da karfin aljihu da sababbin dabaru na tsimi da tanadi da kuma amfani da kudadensu, amma suna bukatar tsarin da zai sada sha’aninsu na kudi da ayyukan kiwon lafiya, da harkokin nishadi, da kuma more rayuwarsu a manyan wuraren kulawa da dattawa.
Wani bincike na baya-bayan nan da aka gudanar ya nuna cewa kashi 70 cikin 100 na wadanda aka ji ta bakinsu sun nuna bukatar ganin bankuna suna taimakawa wajen samun ayyukan kiwon lafiya cikin sauki, yayin da kusan kashi 60 cikin 100 kuma suke sha’awar ganin an sada tsakanin harkokinsu na kudi da kuma wuraren kula da rayuwar dattawa.
Bankunan sun fara duba wannan bukata, inda yanzu haka Bankin CCB na kasar Sin ya muhimmanta ba da fifiko ga dattawa a tsare-tsarensa na bayar da bashi, yayin da Bankin masana’antu kuma ya fitar da wata takardar bayani da ke bayyana karin kebabbun hidimomin kudi ta amfani da shafin intanet da sauran hanyoyi na zabi da suka shafi kula da sha’anin dattawa.
Sakon hakan dai a bayyane yake, ma’ana, cire fargaba kan sha’anin kudin dattawa da kuma samar da ingantattun tsare-tsare masu tallafa wa rayuwar dattawa ta hanyar samun koshin lafiya, da aminci mai gamsarwa a shekarunsu na tsufa.
Tabbas, a yayin da kasar Sin ke dab da fara aiwatar da shirin bunkasa ci gaban kasa da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, nasarar wadannan tsare-tsare za ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar kula da kudaden dattawa yadda ya kamata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link