Mutane Da Dama Sun Rasu Bayan Tashin Bam A Masallaci A Borno
Ana fargabar mutane da dama sun mutu, yayin da wasu da yawa suka jikkata bayan tashin wani bam a wani masallaci da ke Gamboru Kasuwa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, da yammacin ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake yin sallar Magariba a masallacin, kamar yadda shaidu suka tabbatar.
- ’Yansanda Sun Kama Mutum 20 Kan Zargin Aikata Laifin Fyaɗe Da Fashi Da Makami A Katsina
- ‘Yan Majalisar Kano 2 Sun Rasu A Rana Ɗaya
A halin yanzu, babu wani cikakken bayani kan harin bam ɗin ba, ciki har da adadin waɗanda suka rasu ko suka jikkata, domin jami’an tsaro sun kulle yankin.
Har zuwa lokacin dhaɗa wannan rahoto, sojoji ko ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.
Cikakken bayani na tafe daga baya…