Haɗin Gyaran Mace

[ad_1]

Wannan haɗin yana da matuƙar kyau sosai yana gyara mace duk yadda ta kai zai dawo mata da martabarta.

Abubuwan da ake buƙata:

Kankana, Kokumba, Tumatir, Mazarƙwaila, Madara Peak, Dabino.

Yadda ake haɗawa:

  • Yadda Za A Hada Maganin Cutar Ciwon Sanyi Ko Wane Iri
  • Illar Kari (Fibroid) Da Kuma Maganinsa

A yanka kankana duka a haɗa da ƴaƴanta, ita ma kokunban duka za a yanka har da bayan, kada a cire ƴaƴan, a yanka tumatir shi ma kada a matse ruwan cikinsa sai ki daka kanunfari ki jiƙa dabinon, ki cire ƙwallayen ki haɗe su wuri ɗaya, ki markaɗa Bilanda, sai ki juye ki saka mazarƙwailar ta narke ki zuba zuma sai ki juye madarar peak ɗaya.

Ki riƙa sha safe da yamma za ki sha mamaki Hajiya.

Waɗannan abubuwan suna da kyau mata su riƙa amfani da su domin gyaran jiki da kuma samun Isasshiyar lafiya a jikinsu.

  1. Ruwan Abarba: Yana da kyau mace ta riƙa markaɗawa tana tacewa tana sha da suga ko zuma, wannan haɗin yana gyara mace sosai da sosai.
  2. Rake: Shi ma tana gyara mace kuma yana da amfani matuƙa a jiki, domin yana gyara mace sosai da sosai.
  3. Aya: Ita ma duk tafiyarsu ɗaya da rake, Ayar ana so irin ɓula-ɓular nan tana da matuƙar muhimmanci a wurin mace tana gyara sosai, kuma za’a iya samun kunun aya a haɗa shi da madarar peak ta ruwa.
  4. Zaitun: Man zaitun yana magunguna da yawa, to ana so mace ta riga shafa shi ajikinta yana gyara fata da saka santsin jiki, haka ma yana da kyau mace ta dinga shafawa domin gyara saboda yana saka laushi.
  5. Ɓawon Bagaruwa: Ita kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a gyare ta dinga dafa ɓawon tana shiga kamar yadda ake shiga ruwan ɗumi idan an haihu.
  6. Ga kuma wani haɗi a nemi sasaƙen ɓaure, kanunfari, zuma, citta, mazarƙwaila. Za ki tafasa sasaƙen ɓaure ya dahu sosai sai ki daka kanumfari me yawa da citta yar kaɗan ki zuba a kai, ki saka mazarƙwailar da zuma, amma za ki cire itacen kafin ki zuba haɗin, sai ki sauke ki dinga sha daidai kima idan ya huce, wannan haɗin kaɗai ya ishi mace, ba sai ta wahalda kanta neman boka ko wani asiri tana raba kanta da Allah ba.
  7. A samu zogale a wanke shi a niƙa shi tare da dabino da kuma kwakwa sai a tace a saka zuma tare da madara sai a saka ya yi sanyi a riƙa sha bayan mangariba.
  8. Wannan haɗin shima yana gyara mace, niƙaƙƙen riɗi gari, dabino, madara ta ruwa a haɗa su wuri guda a dama namiji zai sha mace ma za ta sha.
  9. Ina mata masu fama da matsalar bushewar gaba? ki samu man riɗi ki riƙa zubawa cikin ruwan ɗumi ki zauna a ciki, sannan ki riƙa matsi da Albabunaj ko Hulba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *