An kashe dan Najeriya da ke taya Rasha yaki da Ukraine
[ad_1]
Wani dan Arewacin Najeriya ya mutu a fagen daga a yayin da yake taya sojojin kasar Rasha yaki da Ukraine.
A ranar Litinin ne dan jarida Jaafar Jaafar da mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, suka tabbatar da wannan labari.
Makama ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya ce mutumin ya bar iyalansa a Arewacin Najeriya ya tafi ya shiga rundunar sojin Rasha domin yaki da Ukraine.
“Abin bakin ciki. Ya bar iyalansa a Arewacin Najeriya ya shiga rundunar sojin Rasha domin yaki da Ukraine. An kashe shi a fagen daga,” in ji Zagazola Makama.
Ya zuwa yanzu, yakin da ya fara tun watan Fabrairu 2022 bayan mamayar Rasha a Ukraine, ya shiga shekara ta hudu.
Yakin ya riga ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilasta miliyoyin ’yan kasar Ukraine barin gidajensu.
Rasha na fama da karancin ma’aikata a fagen yaki, lamarin da ya sa ta dogara da daukar ma’aikata daga kasashen waje, masu zaman kansu da kuma kungiyoyin mayaka domin ci gaba da yakin.
Wannan labari ya sake jaddada yadda rikicin Ukraine da Rasha ke ci gaba da shafar rayukan mutane daga sassa daban-daban na duniya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link