Sojoji sun biya Sakkwatawa diyyar harin jirgin yaƙi

[ad_1]



Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta biya diyyar mutanen da harin jirgin yaƙi ya shafa a bisa kuskure a ranar 25 ga Disamba, 2024, a Jihar Sakkwato.

Waɗanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa da ke Karamar Hukumar Silame a jihar.

Daraktan yaɗa labarai na NAF, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya sanar a ranar Lahadi a Abuja, cewa  Shugaban Rundunar Sojin Sama, Iya Mashal Sunday Kelvin Aneke, wanda ya samu wakilcin Shugaban Hulda da Jama’a tsakanin Sojoji da Fararen Hula, AVM Edward Gabkwet, ya yi bayani kan yadda lamarin ya faru.

Ya ce harin jirgin, ya kasance karkashin rundunar Operation Fasan Yamma, bayan samun rahotannin leƙen asiri da suka nuna cewa akwai ‘yan ta’adda da ake zargi suna ƙetarawa ta cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Duk da cewa rahotanni da dama na leƙen asiri sun tabbatar da hakan, san samu takardar ƙorafin a watan Afrilu 2025 cewa an kashe  fararen hula a harin.

“Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa an aka fararen hula 13 bisa kuskure, wasu takwas sun samu raunuka iri-iri.

“Wannan sakamakon ya matuƙar taba zuciyar rundunar, kuma ya sa aka ɗauki matakan gaggawa domin gyara kura-kuran da aka samu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa da kuma jajantawa, a kawo batun tabbatar da gaskiya da riƙon amana, rage tashin hankali, da kuma kawo karshen rudani.

Haka kuma, matakin zai taimaka wa rundunar wajen ɗaukar darasi mai muhimmanci domin rage yiwuwar faruwar irin wannan kuskure a nan gaba.

Shugaban rundunar ya sake jaddada kudirin rundunar na yin amfani da ƙarfi cikin tsari da daidaito wajen kawar da ’yan ta’adda da sauran miyagu a kasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *