An sake ceto ɗalibai 130 da aka sace a Neja
[ad_1]
Ƙarin wasu ɗalibai 130 na makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, a Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jihar Neja, sun kuɓuta daga ’yan bindiga.
Har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka sake su.
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Sunday Dare ne, ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar Lahadi.
“An saki ƙarin ɗaliban Jihar Neja 130 da aka sace. Babu ko guda ɗaya da ya rage a hannun masu garkuwa da mutane,” in ji shi.
A baya, jami’an tsaro sun samu nasarar ceto ɗalibai 100 a ranar 8 ga watan Disamba.
Hakan ya kawo adadin ɗaliban da aka kuɓutar zuwa 230.
An sace ɗaliban ne a ranar 21 ga watan Nuwamba, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari makarantar da misalin ƙarfe 2 na dare a kan babura.
Lamarin ya tayar da hankali game da ƙaruwar matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.
Daga bisani, Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta bayyana cewa yara 50 sun tsere a lokacin harin.
Bayan sace ɗaliban, Shugaba Bola Tinubu, ya umarci a tura sojoji a ƙasa da kuma sanya ido ta sama a jihohin Neja, Kebbi da Kwara domin bin diddigin masu garkuwa da mutane.
Bayan ɗaukar wasu matakai, an rufe wasu makarantu na Gwamnatin Tarayya, jihohi da sauran cibiyoyi da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link