‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Bisa Zargin Luwaɗi Da Ƙananan Yara A Bauchi
Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta cafke wasu matasa guda biyu bisa zarginsu da cin zarafin wasu ƙananan yara ta hanyar tursasawa wajen yin Luwaɗi da su a Tilden Fulani da ke ƙaramar hukumar Toro ta jihar.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Nafiu Habib, ya fitar a jiya, wani mahaifin da lamarin ya tada wa hankali ne ya kai rahoton faruwar lamarin a ranar 8 ga Janairu, 2026, zuwa ga shalkwatar ‘yansanda da ke Tilden Fulani.
- Duk Da Rashin Nasara A Hannun Morocco, BUA Ya Bai Wa Super Eagles Kyautar Dala 500,000
- Sabuwar Yarjejeniyar FGN-ASUU: Tinubu Ya Amince Da Ƙarin Sabon Alawus Ga Farfesoshi
Mai ƙorafin ya yi zargin cewa wani matashi mai shekaru 16, mai suna Mohammed Saifullahi (wanda ake zargi) shi ne ya yaudari ɗansa mai shekaru 8 (an ɓoye sunansa) har ya yi masa Luwaɗi da ƙarfin tsiya.
A cewarsa, Saifullahi ya yi amfani a lokuta da dama da alewa da aya wajen janyo hankalin yaron domin ya yaudari shi don samun damar yin Luwaɗi da shi, lamarin da ya sanya ake zargin Saifullahi da cin zarafin yaron.
SP Habib ya ce bayan karɓar rahoton, nan take aka tura jami’an bincike zuwa yankin. An kama wanda ake zargi, yayin da aka garzaya da yaron da abin ya shafa zuwa asibiti domin duba lafiyarsa da kula da shi.
Ya ƙara da cewa, yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shafe sama da shekaru uku yana aikata irin wannan ɗanyen aikin na Luwadi, kuma ya ayyana sunan wani matashin Shuaibu Sulaiman, mai shekaru 17 a matsayin abokin cin burminsa.
A cewar sanarwar ‘yansandan zuwa yanzu dukkanin waɗanda ake zargin mutum biyun Saifullahi da Sulaiman duk suna tsare a hannun ‘yansanda.
Binciken farko na ‘yansanda (POI) ya kuma gano cewa wanda ake zargi na farko ya taɓa cin zarafin ƙananan yara huɗu masu shekaru tsakanin 7 zuwa 10.
“Saboda haka, duk mutanen da aka kama sun amsa laifinsu,” in ji kakakin ’yan sandan, yana mai ƙara da cewa bincike na ci gaba da gudana. Ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da wannan aiki tare da gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci kowace irin cin zarafi ga yara ba.
Ya kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su kasance masu sa ido sosai tare da lura da harkoki da motsin ’ya’yansu domin hana aukuwar irin waɗannan abubuwan a nan gaba.