Gwamnatin Tarayya ba ta biyan ’yan bindiga kuɗin fansa — Ministan Tsaro

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada matsayinta cewa ba ta biyan kuɗin fansa ga waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ta ce jami’an tsaro suna dogaro ne da matsin lambar soja da kuma ayyukan leƙen asiri wajen kubutar da waɗanda aka sace.

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana haka a cikin wata hira da BBC Hausa ta yi da shi a Kaduna, yayin da ake ta zargin cewa ana biyan kuɗin fansa domin a saki waɗanda aka yi garkuwa da su, musamman daliban makarantu.

Ya ce: “Gwamnatin tarayya ba ta biyan kuɗin fansa. Ko da wasu suna yi, gwamnati ba ta yi. Ba mu biyan kuɗin fansa,” in ji Musa.

Ya jaddada cewa yawancin waɗanda aka kubutar ana samun nasarar sako su ne bayan muhimman ayyukan tsaro.

Ya ce: “Mutane kawai suna ɗauka ana biyan kuɗin fansa. Misali, duk lokacin da aka yi garkuwa da yara daga makarantu, sojoji kan shiga daji su matsa wa ’yan ta’adda har su gudu su bar yaran, sannan mu kwaso su. Babu batun biyan kuɗin fansa,” in ji shi.

Musa ya gargadi cewa biyan kuɗin fansa yana ƙarfafa ’yan ta’adda kuma yana ƙara yawan garkuwa da mutane.

Ya ce: “Ba ma son hakan, domin idan aka ci gaba da biyan kuɗin fansa, zai ƙara ƙarfafa mutane su rika yin garkuwa da mutane don karbar kuɗi. Shi ya sa muke cewa a daina biyan kuɗin fansa,” in ji shi.

Ya shawarci iyalai da al’umma su rika sanar da hukumomin tsaro idan an yi garkuwa da danginsu, maimakon yin tattaunawa da masu garkuwa.

Ya ce: “Idan aka yi garkuwa da wani, ya kamata a sanar da jami’an tsaro domin a ɗauki matakin da ya dace,” in ji ministan.

Ministan tsaron ya kuma gargadi al’umma da su daina hulɗa da ’yan ta’adda, ciki har da sayar musu da abinci da sauran kayayyaki.

Ya ce: “Muna ta gaya wa mutane su daina hulɗa da ’yan ta’adda, su daina sayar musu da abinci ko abin sha,” in ji shi.

Musa ya yi kira da a ba jami’an tsaro haɗin kai, yana mai cewa bayanan sirri daga ’yan ƙasa suna da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *