Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda
[ad_1]
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku da aka gudanar a Katsina.
Radda, ya karyata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yada cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ’yan bindigar da ke ɓoye a dazuka.
A cewarsa: “Babu wata tattaunawa ko sasanci da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda. Wadannan labarai ƙarya ne, kuma manufar gwamnati ita ce kawo ƙarshen ta’addanci, ba yin sulhu ba.”
Sai dai ya ce, gwamnati za ta iya rungumar zaman lafiya idan waɗannan mutane sun yi tuba na gaskiya, tare da miƙa wuya, suka daina zubar da jini.
Gwamna Radda, ya bayyana cewa horar da jami’an CWC wani ɓangare ne na sabuwar dabarar gwamnati ta inganta tsaro, musamman a yankunan karkara da suka fi fama da hare-haren ’yan ta’adda.
Tun bayan ƙaddamar da Katsina jami’an tsaron a shekarar 2023, an horar da dubban matasa sama da 2,400 daga sassa daban-daban na jihar.
Wadannan jami’ai na aiki tare da ’yan sanda, sojoji, da jami’an Sibil Difens, don taimakawa wajen samun bayanan sirri da hana hare-haren ’yan ta’adda.
Gwamnan, ya ce horar da waɗannan jami’ai zai taimaka wajen kawo ƙarshen satar mutane da hare-haren ’yan bindiga, tare da tabbatar da zauna lafiya a Jihar Katsina.
Ya kuma yi kira ga al’umma su bai wajami’an tsaro haɗin kai, su rika bayar da bayanai domin ganin an samu nasara a yaki da ta’addanci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link