Ƴan Bindiga 10,000 Sun Tarwatsa Ƙauyuka A Bauchi

[ad_1]

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa sama da ‘yan bindiga 10,000 ne suka tarwatsa wasu ƙauyuka a jihar, lamarin da ya tilasta neman gaggawar tallafin Gwamnatin Tarayya domin daƙile barazanar tsaro.

Gwamnan ya ce hare-haren sun haddasa asarar dukiyoyi da kuma raba al’umma da muhallansu, yana mai jaddada cewa ƙarfin da ake fuskanta ya wuce abin da jihar za ta iya tinkarawa ita kaɗai

  • Hedikwatar Tsaro Ta Tabbatar Da Isowar Sojojin Amurka A Jihar Bauchi
  • Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Jaridan Bauchi Sun Yi Hatsari Yayin Ɗaukan Rahoton Ayyukan NEDC

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara tura jami’an tsaro da kayan aiki na zamani domin murƙushe ‘yan bindigar da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Bala Mohammed ya kuma yi kira ga al’umma da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Bauchi

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *