Fintiri Ya Fice Daga PDP Zuwa APC
[ad_1]
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, yana mai cewa matakin na da muhimmanci ga makomar jihar.
A jawabin da ya yi wa al’ummar jihar safiyar Juma’a, Fintiri ya ce sauyin ya biyo bayan tuntuɓa mai zurfi da ɓangarori daban-daban na jama’a, tare da bayyana cewa yanayin siyasar ƙasa na buƙatar matakai masu tsauri da hangen nesa.
- Sojoji Sun Daƙile Hare-Haren Ƴan Ta’adda, Sun Kwato Makamai A Borno Da Adamawa
- ‘Yan Majalisar Dokokin Adamawa 6 Sun Fice Daga Jami’yyar PDP
Ya ce daidaita Adamawa da APC zai bai wa jihar damar tallafa wa ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ke mayar da hankali kan walwala, ababen more rayuwa, gidaje da ci gaban tattalin arziƙi mai haɗa kowa.
Gwamnan ya jaddada cewa matakin bai samo asali daga muradi na ƙashin kai ba, illa domin ɗorewar ci gaba da zaman lafiyar jihar, yana mai cewa za su koma APC da dukkan ƙananan hukumomi 21, gundumomi 226 da dukkan zaɓaɓɓu da naɗaɗɗun muƙarrabansu.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa su shiga APC tare da yin rajista da yawa domin tunkarar makoma da ya bayyana a matsayin tabbatacciya.
[ad_2]
Source link