An Nemi A Yi Hattara Da Guguwar Sauya Sheƙar Siyasa Da Ta Kama Jihar Adamawa
Wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Adamawa ya yi kira ga jagororin jam’iyyar na ƙasa da su yi takatsantsan a kan shirin da ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP suke yi na tururuwar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a jihar, saboda a cewarsa shirin su na dawowa jami’yyar APC yana iya kassara jam’iyyar tare da cutar da asalin yan jam’iyyar da suka yi wa jam’iyyar bauta na shekara da shekaru.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Sanata Abdurrahaman Buba Kwacham, Sarkin Fulanin masarautar Mubi kuma shugaban ƙungiyar matasan Arewacin Nijeriya a hirarsa da manema labarai a Abuja.
- Ƙoƙarin Amurka Na Ganin An Haramta Shari’a A Nijeriya Ya Haifar Da Cece-kuce
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 9
Ya ce ba wai yana yaki da shugowar Gwamna Fintiri da jama’arsa suke ƙoƙarin yi ba ne amma ya kamata a tabbatar da cewa, shigowarsu bai danne ‘yan asalin jam’iyyar ba waɗanda suka yi azumin fiye da shekara 8 ba tare da an dama da su ba.
Ya kara da cewa, tsarin jam’iyyar APC na cewa, Gwamna ne shugaban jam’iyya a jiha ko da kuwa yanzun nan ya shigo jam’iyyar abu ne da ya kamata a yi watsi da shi, domin babu adalci an ciki, “Ba gwamna kadai a ke buƙata ba a wajen cin zaɓe ba, dole a tabbatar ana tafiya tare da talakawa masu kada ƙuri’a, saboda haka ya kamata a samar da ƙofar da suma za su san ana yi da su” in ji shi.
A kan haka ya buƙaci a gaggauta soke dokar domin hakan zai iya kawo wa jam’iyyar cikas wajen cin zaɓe, “Mun ga irin haka a Jihar Zamfara inda Gwamna Dauda Lawal ya kayar da gwamnan da ke kan kujerar mulki”.
Daga nan ya yi watsi da masu yada cewa, yana adawa ne da shigowar Gwamna Fitiri jam’iyyar APC saboda yana fargabar ko Gwamna zai iya neman takarar kujerar Sanata a yankin Adamawa ta tsakiya, inda shima daga nan ya fito, kuma ana raɗe-raɗin zai tsaya takarar kujerar sanata “Bana tsoron fuskantar kowa a fagen zabe musamman ma da a yanzu dokar zaɓe ta soke tsarin DELIGET wajen fitar da dan Takara a zaɓukan cikin gida na jam’iyyu.
“Ina da yakinin talakawa na tare dani, kuma shune za su fitar da dan takara a dukkan matakai, wannan karon babu batun kashe kuɗi domin sayen deliget kamar yadda ‘yan siyasa suka rinƙa yi a baya” in ji shi.
Daga ƙarshe Sanata Buba Kwacham ya nemi ‘yan siyasar Jihar Adamawa su haɗa kai tare da kai zuciya nesa domin tabbatar da zaman lafiya tare da kuma gudanar da siyasa mai tsafta.