Tsoffin Kwamishinoni sun maka Gwamnatin Kano a kotu kan ƙwace musu motoci
[ad_1]
Tsofaffin Kwamishinoni biyar ciki har da ɗan jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, sun maka Gwamnatin Jihar Kano a kotu kan ƙwace motocin da suke amfani da su lokacin da suke riƙe da muƙamai.
Aminiya ta ruwaito cewa Hukumar Ƙarbar Ƙorafe-ƙorafe ta jihar (PCACC), ta je gidajen tsofaffin kwamishinonin tare da ƙwato motocin, bayan ta buƙaci su mayar da su.
Tsofaffin kwamishinonin sun haɗa da Nasiru Sule Garo, AVM Ibrahim Umar, Adamu Aliyu Kibiya, Yusuf Ibrahim Kofar Mata, da Mustapha Rabiu Kwankwaso.
Sun yi murabus ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.
Takardun kotu sun nuna cewa Ibrahim Umar ya shigar da ƙara yana zargin jami’an PCACC sun shiga gidansa a ranar 26 ga watan Fabrairu, inda suka tayar wa iyalansa hankali tare da ƙwace motarsa.
Yana roƙon kotu ta bayar da umarnin a mayar masa da motar tare da bayyana jami’an da suka shiga gidan.
A wata sanarwa da tsofaffin kwamishinonin suka fitar tare, sun zargi gwamnati da ƙoƙarin tsoratar da su.
Sun ce motocin aiki na daga cikin haƙƙoƙinsu na ofis, don haka bai kamata a ƙwace su ba.
Sun kuma ce an kwashe motocin matansu lokacin da ba sa nan.
Sun bayyana cewa an keta ’yancinsu da mutuncin iyalansu, suna mai cewa an yi hakan ne domin kunyata su da kuma hana su adawa da gwamnatin.
Shugaban PCACC, Saidu Yahaya, ya ce sun ƙwato motocin ne bisa umarnin kotu bayan tsofaffin Kwamishinonin sun ƙi mayar da su.
Sai dai tsofaffin kwamishinonin sun ce kotu ce kawai ta ke da hurumi, tare da roƙon magoya bayansu su kwantar da hankalinsu.
Lamarin ya ƙara dagula yanayin siyasa a Kano, bayan sauya sheƙar gwamnan da kuma murabus ɗin mambobin majalisar zartarwa.
Lamarin ya ƙara haifar sanya adawa mai zafi tsakanin APC mai mulki da magoya bayan Kwankwasiyya a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link