Tinubu Ya Yi Alƙawarin Ƙara Ƙaimi Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro

[ad_1]

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar, yana mai jaddada cewa kare lafiyar ‘yan Nijeriya da walwalar su na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa gaba.

Ya kuma yi gargadin cewa rikicin da ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya na iya haifar da sabon hauhawar farashin kaya wanda ka iya barazana ga tattalin arzikin ‘yan kasa.

  • 2027: Cikin Ƴan APC Ya Ɗuri Ruwa Saboda Tasirin Makinde  – Ƙungiyar PDP
  • Kano Pillars Ta Doke Enyimba, Ta Matsa Gaba A Teburin Gasar NPFL

Yayin da yake jawabi a wajen taron Eid-el-Fitr da aka gudanar a gidansa da ke Legas, inda ya karɓi baƙuncin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da gwamnoni 23 na jihohi, Tinubu ya yi kira da a haɗa kai wajen yaƙar ayyukan ta’addanci.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, wadda mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ya bayyana cewa ziyarar aikibda ya yi kwanan nan a kasar Ingila ta mayar da hankali ne kan samar da ingantattun kayan aiki da tallafin tsaro.

Ya ce, “Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da muka tattauna a Ingila shi ne batun kayan aiki da tallafi. Zan iya sanar da ku cewa jiya ma, na sake yin wata doguwar tattaunawa da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron. Muna haɗa kai da su wajen samar da kayan aiki da tallafi. Ina kuma yin ƙoƙari matuƙa wajen tuntuɓar sauran ƙasashe.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *