Jerin matsaloli 7 da ke addabar Mayankar Gombe
[ad_1]
Mahauta a Jihar Gombe sun bayyana damuwa kan tarin matsalolin da ke addabar mayankar dabbobi, musamman rashin ruwa, wutar lantarki da kuma tsafta, waɗanda ke kawo cikas ga ayyukansu da kuma barazana ga lafiyar jama’a.
Matsalar Ruwa Na Dagula Sana’a
Tsohon shugaban ƙungiyar masu yanka dabbobi, Alhaji Kabiru Bala Onye, ya ce rashin ruwa na tilasta musu sayen ruwa wajen ’yan ga ruwa domin tsaftace nama da wuraren aiki.
Ya ce hakan na ƙara musu kashe kuɗi kuma ya rage ribar da suke samu. Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa rashin ruwa na iya haifar da cututtuka irin su kwalara da typhoid sakamakon rashin tsafta.
Rashin Kula da Tsafta
Kabiru ya koka kan yadda mayankar ke cike da datti, jini da kashin dabbobi da ake zubarwa ba tare da kulawa ba.
A cewarsa, hakan na haddasa wari da yaɗuwar ƙwari, lamarin da ke barazana ga lafiyar jama’a, musamman duba da cewa wurin yana da alaƙa kai tsaye da abincin da ake ci.
Rashin Wuta Da Barazanar Tsaro
Rashin wutar lantarki a mayankar ya zama babbar matsala, inda wurin ke kasancewa cikin duhu musamman da sassafe da kuma da daddare.

Ya ce hakan na jefa ma’aikata cikin haɗarin tsaro, tare da ba masu aikata laifi damar kai hari ko satar kayayyaki. Bugu da ƙari, rashin wutar lantarki na hana amfani da na’urorin sanyaya nama, wanda ke haddasa asara.
Lalacewar Gine-Gine
Shi ma shugaban ƙungiyar mahauta ta jihar, Suleiman Umar Chansa, ya bayyana cewa mayankar na cikin mummunan hali, inda wani sashi na katangar wurin ya rushe.
Ya ce hakan na bai wa bata-gari damar amfani da wurin a matsayin mafaka, yayin da rashin magudanan ruwa ke ƙara ta’azzara matsalar tsafta.
Asarar Nama Saboda Rashin Wurin Ajiya
Chansa ya ƙara da cewa rashin wutar lantarki da kayan ajiya na sanyaya nama na jawo musu asara mai yawa, musamman waɗanda namansu ya yi kwantai ba a sayar ba.
Ya ce suna buƙatar a samar musu da dakin sanyaya nama (cold room), ko da ta hanyar bashi, domin rage asarar da suke yi.
Buƙatar Tallafin Gwamnati
Mahautan sun ce duk da suna biyan haraji, ba sa samun isasshen kulawa daga gwamnati. Sun buƙaci a samar musu da rijiyar burtsatse da fitilun hasken rana domin magance matsalolin ruwa da na tsaro.
Sun kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su duba halin da mayankar ke ciki domin kare lafiyar jama’a.
Maƙwabta sun Koka
Wasu mazauna yankin kusa da mayankar sun koka kan wari da gurɓatar muhalli da ke fitowa daga wurin.
Wani mazaunin yankin, Malam Haruna Ali, ya ce wari na hana su numfashi yadda ya kamata, tare da haddasa wa yaransu cututtuka.
Gargaɗin Kwararru
Wani likitan dabbobi da ya nemi a sakaya sunansa ya yi gargaɗin cewa halin da mayankar ke ciki na iya jawo yaɗuwar cututtuka daga dabbobi zuwa mutane.
Ya ce dole ne a kula da tsafta da lafiyar nama kafin a kai kasuwa domin kare lafiyar jama’a.
Shirin Gina Sabuwar Mayanka
A wani ɓangare, gwamnatin Jihar Gombe ta rattaba hannu kan yarjejeniyar naira biliyan uku domin gina sabuwar mayankar dabbobi ta zamani.
An ce aikin, wanda kamfanin Lubel Nigeria Limited zai gudanar, na ƙarƙashin shirin World Bank na L-PRES.
Fatan Samun Sauyi
Shugaban shirin a jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya ce sabon aikin zai inganta tsafta da sarrafa nama bisa ƙa’idojin duniya.
Ana sa ran sabuwar mayankar za ta rage asara, inganta lafiyar jama’a da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Sai dai mahauta sun buƙaci gwamnati da ta gaggauta aiwatar da aikin tare da gyara tsohuwar mayankar domin rage wahalhalun da suke fuskanta.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link