Wata cuta ta kashe gomman damisoshi a Thailand
[ad_1]
Wata mummunar ƙwayar cuta ta yi ajalin aƙalla damisa 72 a wani gandun dabbobi na masu zaman kansu a Arewacin Thailand kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Ofishin kula da kiwon dabbobi na lardin Chiang Mai ya ce gwaje-gwaje sun gano cewa ƙwayar cutar canine distemper mai yaɗuwa sosai, tare da wasu ƙwayoyin bacteria da ke shafar numfashi ce ta kashe damisoshin a cikin makonnin baya-bayan nan.
Da yake zantawa da kafafen labarai na cikin gida, Daraktan Hukumar Kula da Dabbobi ta Ƙasa, Somchuan Ratanamungklanon, ya bayyana cewa, “idan damisa ta kamu da rashin lafiya, ba kasafai ake gano hakan da wuri ba kamar yadda ake gani a karnuka ko kuliyoyi.
“Saboda haka lokacin da muka gano sun kamu, tuni an riga an makara.”
Kungiyar kare haƙƙin dabbobi ta PETA Asia ta ce, “Waɗannan damisoshin sun mutu kamar yadda suka rayu cikin ƙunci da wahala da razanaswa.”
Ta ƙara da cewa idan masu yawon buɗe ido suka daina ziyartar irin waɗannan wurare, kasuwancinsu zai rushe, kuma irin wannan masifa ba za ta riƙa faruwa ba.
Sai dai gandun dabbobin da lamarin ya faru, wato Tiger Kingdom, ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa ranar Asabar kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link