Sojoji Sun Dakile Harin ISWAP Da Boko Haram A Borno
[ad_1]
Sojojin Rundunar Hadin Gwiwa, Operation HADIN KAI, sun dakile harin da ake zargin ‘yan Boko Haram da ISWAP ne suka kai a kauyuka Pulka da Mandaragirau na Jihar Borno.
A cewar wata sanarwa da Jami’in Sadarwa na Operation HADIN KAI, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, harin ya faru a ranar Asabar, lokacin da ‘yan ta’addan suka yi kokarin mamaye matsugunan sojoji a wuraren biyu.
- Sin Ta Ba Da Shawarar Tsayawa Kan Ra’ayoyin Bai Daya Guda Biyar Don Warware Rikicin Sudan
- Hukumar RUWASSA Ta Kudiri Aniyar Samar Da Ruwa A Fadin Jihar Katsina
Sojoji sun bayyana cewa ‘yan ta’addan da ke ci gaba daga yankin daji na Sambisa sun kai mummunan harin kan sojojin Sashen 1 a Pulka. Duk da haka, sojoji sun fafata da masu kai harin da aka bayyana da yaki mai tsanani, inda suka sami nasarar dakile harin da kuma mayar da ‘yan ta’addan baya.
Sanarwar ta kara da cewa, kodayake an samu wani Bangare na shingen tsaro da aka dan karya na dan lokaci wanda ya haifar da lalacewar wasu kayan yaki da wuraren masauki, saurin karin sojoji daga rundunar 26 Brigade ya tilasta ‘yan ta’addan su janye zuwa yankin Sambisa.
“Sahihin Bincike ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun yi asarar rayuka sosai, ciki har da babban kwamanda da aka gano mai suna Abou Aisha wanda ya samu mummunan raunin bindiga a wuya har ya rasu, tare da babbar asarar makamai da kayan aiki,” in ji sanarwar.
Sojojin sun kara da cewa babu wani dan soji da ya rasa ransa yayin fafatawar a Pulka.
A wani labari da ya shafi wannan, an ruwaito cewa sojojin Sashen 2 a Mandaragirau sun shiga wani harin da aka tsara sosai daga Bangarori da dama da ‘yan ISWAP suka kai, wadanda suka hau manyan motoci masu makami da babura. Sanarwar ta bayyana cewa sojoji sun tsara kungiyoyin yaki a wuraren da suka dace domin dakile irin wadannan hare-hare, inda suka samu nasarar korar masu kai harin bayan doguwar musayar wuta.
Duk da cewa shingen wurin bai karye ba, sojojin sun amince cewa wasu sojoji da mambobin CiBilian Joint Task Force sun rasa rayukansu a wannan karo. Wasu da suka ji rauni an tura su da sashin jiragen sama na Operation HADIN KAI da kuma jiragen sojin kasa zuwa asibitoci domin samun kulawar likitoci.
“Sadaukarwarsu tana nuna manyan dabi’un aiki, jarumtaka, da kwazo wajen kare Nijeriya,” in ji sanarwar.
Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa ayyukan bincike a kan hanyar Kimba sun gano sawun jini, kaburbura kasa da kasa, da kayan da aka bari a wurin, yayin da shaidun gani da ido suka nuna cewa an ceto wasu ‘yan ta’adda da suka ji rauni daga filin fama.
Manyan kwamandojin rundunar sun yaba wa sojojin bisa kwarewa da juriya, inda suka bayyana cewa gazawar hare-haren ya nuna karuwar matsin lamba ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki a Arewa-Maso-Gabas.
Operation HADIN KAI ta sake jaddada kudurinta na tarwatsa kungiyoyin ‘yan ta’adda da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
[ad_2]
Source link