Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Umar Bojude, ya rasu

[ad_1]



Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude.

Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi).

Malamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli.

Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam da dukkanin Musulmi a Gombe da Najeriya baki ɗaya.

“Haƙiƙa rasuwarsa babban rashi ne,” in ji Gwamna Yahaya.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa da rahama, Ya kuma sanya shi cikin Aljannar Firdausi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *