Gwamnan Kano Ya Aike Mutane 1,600 Don Gadin Makarantu
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tura ‘yan sa-kai 1,600 da aka ɗauka aiki zuwa makarantu sakandare a faɗin jihar domin inganta tsaro.
Wannan mataki ya biyo bayan sace ‘yan mata 25 daga makarantar sakandare a Jihar Kebbi a makon nan.
Gwamnan ya bai wa ‘yan sa-kan takardun ɗaukar aiki a ranar Talata, inda ya bayyana cewa aikinsu shi ne kare ɗalibai, malamai da dukiyar makarantu.
Ya ce ba za a samu ilimi ba, inda ba a samu tsaro ba, sannan ya buƙace da su yi aiki cikin tsanaki, ladabi da gaskiya.
Gwamnan ya yaba wa Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare na Jihar Kano saboda gaggauta aiwatar da umarnin gwamnati.
Gwamna Abba ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na yunƙurin gwamnatin wajen tabbatar da tsaron makarantu, hana kai hare-hare, da kuma karfafa gwiwar iyaye cewa ‘ya’yansu za su iya samun ilimi cikin kwanciyar hankali.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ƙara inganta matakan tsaro a dukkanin makarantu da ke faɗin jihar.
[ad_2]
Source link