Abubuwan Da Suka Fi Daukar Hankali A Bangaren Tsaron Nijeriya A 2025

[ad_1]

Yayin da Nijeriya ke shiga shekarar 2026, kasar na shirye-shiryen fuskantar shekarar ta yadda za ta samu nasarar warware abubuwan da suka fi ci mata tuwo a kwarya a bangaren tsaro da sauran bangarori da dama. Shekarar da ta gabata ta kasance mai cike da kalubalen siyasa, tattalin arziki, da sauye-sauyen zamantakewa, inda batutuwa kamar gyaran shugabanci, sake fasalin tattalin arziki, da rashin tsaro suka mamaye al’amuran kasar.

Kokarin gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na magance matsalolin kasar na fuskantar ra’ayoyi al’umma daban-daban. Misali, cire tallafin man fetur an dauke shi a matsayin mataki da ya zama dole don magance rashin tsari a harkokin kudi, amma ya haifar da wahalhalu na tattalin arziki ga yawancin ‘yan Nijeriya. Shekarar 2025, ‘yan Nijeriya sun fuskaci hauhawar farashin kayayyaki abinci, karuwar kudin sufuri, da karin farashin wutar lantarki, wanda ya kara matsa lamba ga al’ummar Nijeriya.

  • Yadda Tsare-tsaren Tinubu Na Fitar Da Kaya Ketare Suka Ƙara Wa NPA Ƙwarin Guiwa
  • Iyalan Sheikh Khalifa Abdulkadir Sun Koka Kan Rashin Sanin Halin Da Yake Ciki

Rashin tsaro shi ne babban kalubalin Nijeriya, yayin yawaitar ayyuka ta’addaci ke ci gaba da guda a wurare daban-daban na kasar wanda ya kasance babban barazana ga hadin kai da ci gaban Nijeriya. Karuwar kungiyoyin da ke da alaka da ta’addanci, kamar irinsu Boko Haram, ISWAP, Lakurawa, ISIS da kuma karuwar fashi da makami a jihohi da dama sun kara ta’azzara a 2025.

A cewar kididdiga, shekarar 2025 an samu yawaitar garkuwa da mutane, inda ake ikirarin cewa an sace miliyoyin ‘yan Nijeriya don karbar kudin fansa ko wasu dalila na ta’addanci, musamman a arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.

Duk da cewa girman wannan adadi ya haifar da muhawara, ko shakka babu kisan gilla na jama’a ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan abubuwan da suka bayyana rashin tsaron a 2025.

Daya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali a wannan shekarar ya faru a ranar 13 ga Yuni a cikin kauyen Yelewata na karamar hukumar Guma ta Jihar Benue, inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a cikin dare wanda ya hallaka kusan mutum 200, wanda galibinsu manoma da ‘yan kasuwa.

A ranar 3 ga Satumba, ‘yan Boko Haram sun kai hari Darul Jamal, wata al’umma da ke kusa da kan iyakar Nijeriya da Kamaru a Jihar Borno. Fiye da mutane 80 ciki har da sojoji biya aka kashe su a yayin harin.

Harin ya zo ba da jimawa ba bayan mazauna yankin sun dawo yankin bayan shekarun da suka yi suna gudun hijira.

A matsayin martani, rundunar sojin saman Nijeriya ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya, wanda majiyoyin soja suka ce sun hallaka daruruwan ‘yan ta’adda.

Kazalika, a Jihar Filato ta fuskanci tashin tashin hankali a 2025, inda adadin mutanen da suka rasu ya wuce 150.

A cikin watan Janairu, ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Mangu, suka kashe kusan mutum 30.

Haka kuma a watan Afrilu, an kai hari kan al’ummomi a Gundumar Bokko wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 53 kuma ya tilasta dubban mutane guduwa daga muhallisu.

A Yuni kuwa, harin da aka kai a kananan hukumar Riyom ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 58 kuma ya tilasta wa mutum 15,000 birin gidajensu.

A ranar 17 ga Nuwamba, ‘yan bindiga sun kai hari makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Maga a karamar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi. An sace dalibai ashirin da hudu a yayin harin da aka kai.

Mataimakin shugaban makaranta, Malam Hassan Yakubu Makuku, an kashe shi yayin da yake kokarin kare daliban. Hukumar tsaro daga baya ta tabbatar da sakin dukkan ‘yan matan da aka sace.

Washagarin ranar, a ranar 18 ga Nuwamba, ‘yan ta’adda sun farmaki cocin Chris Apostolic a garin Eruku da ke karamar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.

Akalla masu ibada takwas ne aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama, ciki har da faston cocin.

A ranar 21 ga Nuwamba, wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai 303 da malamai 12 daga makarantar St. Mary Catholic a Papiri na Jihar Neja.

Shaidun gani da ido sun ce masu kai harin sun iso ne tun da sassafa kuma sun kutsa cikin makarantar.

Dubban dalibai sun samu nasarar tserewa, yayin da sauran wadada aka yi garkuwa da su aka sake bayan tattaunawa da matakan tsaro.

A ranar 21 ga Disamba, hukumomi sun tabbatar cewa dalibai da malamai da aka sace sun samu ‘yanci.

Shekarar ta kare da yin kiran don inganta tattara bayanan sirri, kyakkyawar kariya ga cibiyoyin da suke cikin hadari da kuma cikakken tsarin magance tushen tashin hankali a duk fadin kasa.

Yayin da Nijeriya ta shiga shekarar 2026, abubuwan da suka faru a shekarar 2025 sun kasance gargadi mai karfi game da bukatar dawo da aminci, sake gina amana da hana faruwar rashi tsaro a dukkan fadin kasa, wannan ne ya sa gwamati tarayya da na jihohi suka dauki sabbi matakan shawo ka matsalar tsaro baki daya.

A cikin matakan gwamnatin tarayya ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyi masu rike da makamai a matsayin ‘yan ta’adda.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana manufar yayin wani taron karshen shekara a Abuja.

“Daga yanzu, duk wata kungiya mai dauke da makamai ko mutanen da suke sace ‘ya’yanmu da kai hari ga manomanmu, da kuma tsoratar da al’ummominmu an sanya su a hukumance a matsayi ‘yan ta’adda kuma za a yi masa hukunci a matsayin ‘ya ta’adda,” in ji Idris.

Wannan mataki yana ba hukumomin tsaro damar amfani da cikakkun matakan yaki da ta’addanci, yana karfafa musayar bayanan sirri, kuma yana ba da damar daukar matakan aiki tare.

Idris ya ce aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomi a shekarar 2025 ya kai ga kama wasu daga cikin shahararrun ‘yan fashi, ciki har da shugaban ISWAP a Nijeriya.

A cikin wannan shirin, za a tura masu gadin dazuka da aka horar zuwa yankunan karkara, dazuzzuka, da wurare masu nisa da ake yawan amfani da su a matsayin mafaka ga kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Gwamnati ta jaddada rashin lamuntar sace-sacen mutane da tashin tashin hankali a karkara, tana nufin kwantar da hankalin al’ummomin da abin ya shafa da kuma rushe cibiyoyin masu laifi.

A wani matakin shawo kan matsalar tsaro, shirin kula da gandun daji na Shugaban kasa, Bola Tinubu wanda aka kaddamar a watan Mayu 2025 a matsayin wani bangare na sabbin kokarin gwamnati wajen yakar rashin tsaro a fadin kasa ya fara ba da sakamako mai kyau, inda sama da ‘yansanda gandun daji 7,000 da aka dauka aiki a Nijeriya suka kammala samun horo na tsawon watanni uku cikin nasara.

Ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkoki tsaro (ONSA), wanda ya sanar da wannan ci gaba, ya ce an gudanar da bukukuwan kammala karatu a jihohin Borno, Sakkwato, Yobe, Adamawa, Neja, Kwara, da Kebbi.

A halin yanzu, wasu kwararru kan harkokin tsaro sun yaba da shirin Shugaba Tinubu na tura masu gadin dazuzzuka zuwa dazuzzukan da ba a kula da su a jihohi bakwai, sun ce karewar masu gadin kara ingancin ayyukan tsaro sosai a dazuzzukan.

A yayin da yake magana kan aikin masu tsaro gandun dajin lokacin bikin kammala karatu, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkoki tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya ce za su kula da muhalli na Nijeriya kuma za su zama muhimmin karfi a tsarin tsaron kasa, musamman wajen tallafa wa kokarin hukumomin tsaro wajen dakile masu aikata laifuka na rashin tsaro.

Ya bayyana cewa tsaron gandu dazukan Nijeriya wani yunkuri ne na hadin gwiwar hukumomi wanda aka kafa karkashin dabarun shugabancinsa da jagoranci tare da hadin gwiwar ma’aikatar muhalli ta tarayya.

Ribadu ya ce an tsara su ne ta hanyar aiki tare da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar da ke kula da wurare shakatawa ta kasa.

Ribadu ya bayyana wannan sabon shiri a matsayin mataki mai muhimmanci wajen dawo da tsaro a yankuan da ke fama da hadari.

Ya yaba da gudummawar da jami’an da suka bayar horo daga rundunar sojan Nijeriya da ‘yansandan da DSS da NSCDC da hukumar kula da wuraren shakatawa da hukumar samar da bayanan sirra ta kasa (NIA), da gwamnatocin jihohi bakwai da aka zaba domin yin wannan aikin.

Gwamnatin tarayya da na jihohi sun kara kaimi wajen aiwatar da matakan tsaro da za su taimaka waje shawo kan matsalar tsaro a kasar nan.

Sun kaddamar da ‘yansandan al’umma, masu gadin daji, fasahar leken asiri, kungiyoyin aiki na hukumomi daban-daban da hadin gwiwa don rage fashi da makami, ta’addanci, satar mutane da sauran laifukan tashin hankali.

Daga arewa maso yamma zuwa kudu maso gabas da kudu maso kudu da kudu maso Yamma, gwamnonin sun yi amfani da dabaru na dakile kisan kai a yakunansu.

Sun kara hada kan jami’ai da tattara bayanan sirri da karfafa jin dadin jami’ai da saka jari a cikin ababen more rayuwa don kwantar da hankalin ‘yan kasa da kuma mayar da tsaro a guraren da ba su da aminci.

A matakin tarayya, gwamnatin Shugaba Tinubu ta ofishin NSA ta kaddamar da shirin kula da gandun daji na kasa baki daya don hana kungiyoyin masu laifi samun mafaka a cikin manyan gandun dajin Nijeriya.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso yamma, ya ce gwamnonin Katsina, Kano, Jigawa, Kaduna, Sakkwato, Zamfara da Kebbi sun yanke shawarar daukar cikakken matakin tsaron yankin.

Yayin da yake jawabi a bikin kammala karatun jami’ai masu kula da yankunan jihohi (NWC) guda 2,000, Radda ya ce tsaro ya wuce iyakokin jihohi, yana jaddada cewa kare rayuka da dukiya nauyi ne da kowa ya rataya a wuyasa.

Ya ce Katsina kadai ta tura jami’an tsaro na al’umma 6,696 da aka horar, tare da ba su babura fiye da 1,600 da motocin sintiri 102 na Hilud da motocin daukar sojoji masu garkuwa 21 da kayan yaki 1,500 da bindigogi 2,750.

A Kano, Gwamna Abba Yusuf ya kaddamar jami’an NWC a hukumance, inda ya amince da ware naira miliyan 484 don sayan kayan aiki, ciki har da babura 300 da motoci Hilud 88, yayin da ya karfafa rundunar hadin gwiwar tsaro da karin motoci.

Jihar Kaduna ta dauki hanyoyi da dama karkashin Gwamna Uba Sani, ta sake fasalin hukumar kula da tsaro ta Jihar Kaduna (KADBS), ta dauki karin ma’aikata 7,000, ta karfafa musayar bayanan sirri da kuma sanya tsarin zaman lafiya na Kaduna.

A Jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya dauki matasa kusan 10,000 a karkashin tsarin tsaro na hadin gwiwa wanda ke hada kamfanonin tsaro masu zaman kansu da makarantu da cibiyoyin lafiya.

A Jihar Neja, Gwamna Mohammed Umar Bago ya dauki ma’aikatan tsaro na gandun daji da sake fasalin tsarin domin ya yi daidai da kuma hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *