DSS Ta Kama Jami’inta Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ‘Yar Shekara 16

[ad_1]

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani jami’inta mai suna Ifeanyi Onyewuenyi bisa zargin sace wata yarinya ‘yar shekara 16, Walida Ibrahim, a Jihar Jigawa.

Ana zargin jami’in da tsare yarinyar ba bisa ƙa’ida ba, tilasta mata sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci, sannan ya aure ta ba tare da izinin iyayenta ba.

  • Kuskure Ne Daukar Harkar Fim A Matsayin Sana’a Kadai —Maryam CTV (2)
  • Abubuwan Da Suka Fi Daukar Hankali A Bangaren Tsaron Nijeriya A 2025

Haka kuma, rahotanni sun ce ya yi lalata da ita, wanda ya kai ta ga haihuwa.

Wata kotu a Hadejia ce ta ba da umarnin kama jami’in bayan da lauyoyi suka shigar da ƙara a madadin mahaifin yarinyar, suna neman a yi bincike kan lamarin.

A wata sanarwa, DSS ta ce wannan lamari ya saɓa wa dokokinta da ƙa’idojin aiki na jami’anta.

Ta jaddada cewa ba za ta kare duk wani jami’i da ya aikata laifi ba.

Hukumar ta ƙara da cewa tana ci gaba da bincike, kuma za ta bayyana sakamakon binciken ga jama’a da zarar ta kammala.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *