Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Lalata Sansanonin Ƴan Ta’adda A Borno

[ad_1]

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta bayyana cewa jiragen yaƙinta da ke aiki ƙarƙashin Rundunar Haɗin Gwuiwa ta Operation HADIN KAI sun lalata gine-ginen ƴan ta’adda a yankin Abbaga Jiri da ke cikin Timbuktu Triangle a Jihar Borno, a ranar 8 ga Janairu, 2026. Rundunar ta ce harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da kasancewar ƴan ta’adda da wuraren ajiyar kayan aikinsu a yankin.

Kakakin NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an tura jiragen sama domin sa ido da kai hare-haren da suka dace, inda aka kai farmaki kan wuraren da aka gano. Ya bayyana cewa an tsara aikin ne domin raunana ƙarfin ƴan ta’adda, da hana su samun mafaka, da kuma bai wa sojojin ƙasa damar ci gaba da aiki, tare da bin ƙa’idojin yaƙi da kare fararen hula.

  • Hukumar ‘Yansanda A Borno Ta Kwato Harsasai 912
  • Yadda Yara Suka Kamo Harsasan Harbo Jirgin Sama A Yayin Kamun Kifi A Borno

A cewarsa, an lalata gine-ginen ƴan ta’addan baki ɗaya, lamarin da ya hana su walwala da ƴancin motsi. Haka kuma, an kai wani ƙarin hari da ya hallaka ƴan bindiga da aka hango suna taruwa a wurin. Daga bisani, sojojin ƙasa da suka shiga yankin sun tabbatar da nasarar hare-haren sama da ingancin aikin haɗin gwuiwar sama da ƙasa.

Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce nasarar aikin na nuna ƙudirin NAF na mamaye sararin samaniya domin tallafa wa aiyukan haɗin gwuiwa. Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kai hare-haren da suka dogara da bayanan sirri, tare da matsa lamba ba tare da sassauci ba, har sai an rushe dukkan hanyoyin sadarwa da ayyukan ƴan ta’adda da ke barazana ga rayuka, da dukiya da tsaron Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *