Rikicin Gabas Ta Tsakiya Na Iya Sa A Koma Aiki Daga Gida – Dangote

[ad_1]

Fitaccen Attajirin nan na Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana damuwa kan yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara hauhawar farashin man fetur da kuma kawo rashin tabbas ga tattalin arziƙin duniya.

Dangote ya faɗi haka ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu, a Legas.

  • NPC Ta Yi Rajistar Haihuwa 36,000 A Kano Cikin Watanni 9
  • Kusan Shugabannin Kamfanoni 100 Ne Suka Taru Domin Halartar Dandalin Bunkasa Kasar Sin

Ya ce idan rikicin ya ci gaba, zai iya tilasta wa wasu ma’aikata komawa aiki daga gida, kamar yadda aka yi a lokacin annobar COVID-19, sakamakon ƙarancin mai.

Haka kuma ya yi gargaɗin cewa rikicin na iya ƙara jefa Afirka cikin matsin tattalin arziƙi, musamman ga ƙananan kamfanoni da masana’antu da ke amfani da janareta.

Ya ƙara da cewa ko da yake rikicin bai shafi Nijeriya kai-tsaye ba, hauhawar farashin mai a duniya zai shafi ƙasar.

Dangote ya ce suna fatan a samu mafita cikin gaggawa domin rage illar da rikicin ke haifarwa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *